
Gamayyar Kungiyoyin dake saka ido akan harkokin siyasa a jihar Gombe me suna The Gombe State Coalition of Political Civil Societies and Association ta yi Allah wadai da kalaman dan takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar PDP, Farfesa Isa Ali Pantami.
Kungiyar tace kalaman da Dan takarar yayi a ziyarar da ya kai karamar hukumar Dukku abin damuwa ne kuma ya kamata ya kiyaye.
Kungiyar tace dukka ‘yan takarar ya kamata su kiyaye kalamansu da yanayin ma’amalarsu dan a samu siyasa me tsafta.
Kungiyar tace Jihar Gombe an santa da zaman lafiya da fahimtar juna suna kira ga ‘yan siyasar kada su kawo rudanin da zai canja hakan.