Monday, August 17
Shadow

Wata Sabuwa: An baiwa Ali Nuhu Wa’adi ya fito ya tallata Shugaba Tinubu ko a kwace mukamin da aka bashi

Rahotanni sun bayyana cewa an baiwa Ali Nuhu Wa’adin sati daya ya fito ya tallata Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ko a kwace mukamin da aka bashi.

Daya daga cikin jaruman masana’antar Kannywood ce ta fallasa hakan.

Tace ana zargin Rarara ne ya kai gulmarsa sama cewa baya shiga harkar yiwa shugaba Tinubu yakin neman zabe da yake yi, shiyasa aka saka masa wannan wa’adi.

Karanta Wannan  Ma'aikatan Shari'a zasu tsunduma yajin aikin sai mama ta gani gobe, Litinin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *