
Wasu ‘yan gida daya su 5 sun mutu bayan cin abinci me guba a garin Ogidi, dake karamar hukumar Idemili North ta jihar Anambra.
Mahaifiyar su ma na can kwance rai hannun Allah a Asibiti.
Lamarin ya faru ranar Asabar 3 ga watan Mayu 2025 kuma ya jefa mutanen garin cikin damuwa.
Mahaifin yaran Pa Robinson Aghalu dan shekaru 76 wanda tsohon soja ne yace yaran nasa sun fara amai da ciwon ciki ne bayan cin abincin da mahaifiyarsu ta dafa.
Su 6 ne suka ci abincin kuma guda 5 sun mutu.
Kakakin ‘yansandan jihar, SP Tochukwu Ikenga ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace sun dauki abincin dan zuwa a yi gwaji.