Friday, December 6
Shadow

Za mu kawo ƙarshen Lakurawa cikin ƙanƙanin lokaci- Hedkwatar tsaro

Rundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da ɓullar ƙungiyar lakurawa waɗanda suke tayar da zaune tsaye a tsakanin jihohin Sokoto da Kebbi.

Daraktan watsa labarai na hedkwatar ne ya tabbatar da hakan a Abuja, kamar yadda kafofin watsa labarai suka ruwaito, inda ya ƙara da cewa suna da tabbacin ɓullar ƙungiyar a Sokoto da Kebbi.

Sai dai ya ƙara cewa ƙungiyar ba za ta yi wani tasiri ba, domin a cewarsa sojojin Najeriya a shirye suke, kuma za su ga bayansu cikin ƙanƙanin lokaci.

Lakurawa wata ƙungiya ce ta ƴanbindiga da suka fara addabar mutanen Sokoto da Kebbi, kuma sun fito ne daga ɓangaren yankin Sahel da ya ƙunshi ƙasashen Nijar, da Mali, kuma mutane ne da suka ƙunshi ƙabilu daban-daban na Sahel.

Karanta Wannan  Sarkin Musulmi Ya Karrama Matashi Mai Aikin Shara Da Ya Tsinci Kimanin Naira Milyan 16 Ya Maida A Filin Jirgin Sama Na Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *