Wednesday, May 21
Shadow

Wanda suka yi Gàrkùwà da janar Tsiga a Katsina sun nemi a biya kudin fansa Naira Miliyan dari biyu da hamsin(250m)

Yan Bindigar da suka yi garkuwa da tsohon janar din soja kuma tsohon shugaban hukumar bautar kasa(NYSC) Janar Maharazu Tsiga rtd sun nemi a biya Naira Miliyan 250M a matsayin kudin fansarsa.

Wata majiya dake kusa da iyalan janar dinne suka bayyana hakan inda suka ce masu garkuwa da mutanen sun kira iyalan janar din suka sanar da hakan.

An yi garkuwa da janar tsiga ne tare da wasu mutane 9.

Lamarin ya faru ranar Laraba da dare inda ‘yan Bindiga su kusan 100 suka zagaye gidansa suka tsafi dashi.

Dan majalisar tarayya dake wakiltar Bakori da Danja ya tabbatar da faruwar lamarin saidai zuwa yanzu hukumomin soji dana ‘yansanda basu bayar da ba’a si ba kan lamarin.

Karanta Wannan  Ranar Da Aka Karɓe Ka A Cikin Kwankwasiyya Daga Ranar Za Ka Fara Kirga Asara, A Cire Maka Hula Zanna Ta ₦30,000 A Sa Maka Jar Hula Ta ₦1000, Inji King Indara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *