Tuesday, April 7
Shadow

An kama mutane 2 a jihar Borno saboda Kkashe wata mata bisa zargin Maita

‘Yansanda a jihar Borno sun sanar da kama mutane 2 bisa zargin kisan da sukawa wata mata me shekaru 70 a Biu dake jihar bayan zarginta da maita.

Kakakin ‘yansandan jihar, CP Yusuf Lawan ya tabbatar da faruwar lamarin a sanarwar da ya fitar ranar Asabar, 22 ga watan Fabrairu 2025.

Ya bayyana sunayen wadanda ake zargi kamar haka,Ja’o Muhammad, Idrisa Muhammad, 20, da Ya’u Muhammad, 30. 

Yace matar sunanta Hajara Saleh wadda aka kashe a Bantine dake Biu.

Hukumar ‘yansandan tace mutanen da ake zargin sun hada kai dan kashe Hajara inda suka zargeta da maita da jawowa garinsu bala’i.

Ya bayar da tabbacin hukunta wadanda ake zargin.

Karanta Wannan  Kalli Yanda aka gano wani Kirista da yayi amfani da hoton makabartar Musulmai da cewa Kiristane da aka Shyekye dan ya jawo hankalin kasar Amurka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *