Friday, December 12
Shadow

Kai ba karamin yaro bane, ya kamata ka sawa Zuciyarka dangana akan maganar rasa mukamin Minista>>Tinubu ya gayawa El-Rufai

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya gayawa tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya hakura da maganar rasa mukamin minista wadda an yi tun tuni.

Ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Bayo Onanuga inda yace El-Rufai sai raki yake kamar wani karamin yaro da aka kwacewa biredi.

Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na ChannelsTV.

Onanuga yace kamata yayi El-Rufai ya sakawa ransa dangana ya bar maganar rasa mukamin ministan da yayi.

Onanuga yace yana tausayawa El-Rufai dan ya ga Alamar lamarin ya bata masa rai sosai.

A jiya ne dai El-Rufai a hirarsa da Arise TV ya bayyana cewa, Tinubu ne ya ki bashi minista ba Majalisa ce ta ki amincewa dashi ba.

Karanta Wannan  Saboda Na Ki Amincewa A Dinga Turawa Kwankwaso Naira Bilyan Biyu Duk Wata Daga Ofishina, Shine Mafarin Karan-Tsanar Da Gwamna Da Kwankwaso Suka Dora Min Har Ta Kai Ga Mun Samu Matsalà, Inji Baffa Bichi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *