Thursday, December 18
Shadow

Wannan Tsabar Muguntace, Inji Kungiyar ‘yan kasuwar man fetur masu zaman kansu bayan da Dangote ya rage farashin man fetur dinsa zuwa Naira 740 aka kowace lita

Kungiyar ‘yan Kasuwar man fetur masu zaman Kansu PETROAN ta yi Allah wadai da rage farashin man fetur da Dangote yayi zuwa Naira 740 akan kowace lita.

Dangote ya rage farashinne daga yanzu har zuwa watan Fabrairu.

Inda ‘yan kasuwar suka ce hakan zai sa su rasa Kwastomominsu dakuma tafka asarar Naira Biliyan 100.

Kungiyar tace sabawa doka ne ace mutum daya ne zai rika kayyade farashin man fetur a Najeriya.

Tace a su kadai wannan lamari zai shafa ba haddashi Dangoten.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Rashida Mai Sa'a ta jawo cece-kuce bayan data kawo wani Kwado wanda tace na matan aure ne da mazansu ke bin mata a waje, tace kwadon yana hana Zarmalulun Namiji tashi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *