
A jiyane da muka kawo muku Rahoton cewa, Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo ya kulle kasuwar Onitsha na tsawon sati daya.
Dalili shine ‘yan kasuwar na biyewa tshageran dake hanasu bude shaguna ranar Litinin.
A martanin ‘yan kasuwar, sun je gadar Onitsha inda suka ajiye motocinsu suka hana shiga da fita garin dan nuna fushinsu da matakin da gwamnan ya dauka.