
Rahotanni daga Dutsin Ma ta jihar Katsina na cewa, a cikin watan Azumin Ramadana, Hukumar Hisbah ta jihar ta kama wata mata me shekaru 26 tare da dadironta wanda Kirista ne me shekaru 35 a garin Dutsin ma.
Rahoton yace an kamasu ne suna zaman dadiro a daki daya duk da ana cikin watan Ramadana.
An kamata ne bisa jagorancin Hisbah karkashin shugabanta, Malam Shafi’u Ibrahim.
Rahoton dai yace masoyan na zaunene ba tare da aure ba.