
Tauraron fina-finan Hausa, Ali Nuhu ya bayyana cewa bai taba samun matsala da matarsa ba game da harkar fim ko da ta ganshi yana soyayya da wasu mata a fim ba.
Ali Nuhu yace, dalili shine yana girmama matar tashi kuma itama tana girmamashi sannan kuma wani lokacin ma yana bata labarin fim din ta karanta.