Tuesday, April 14
Shadow

Sai mutanen Arewa sun daina aure barkatai da haihuwar ‘ya’yan da basu iya kula dasu sannan matsalar tsaro zata zo karshe a Najeriya>> Inji Me magana da yawun Ministan Abuja

Babban Hadimin ministan Abuja ta bangaren sadarwa, Lere Olayinka ya soki mutanen, Arewa inda yace yanayin tsarin rayuwarsu ta auren mata barkatai da haihuwar ‘ya’yan da basu iya kulawa dasu ne ke kara rura wutar matsalar tsaron

Yace ta yaya me gadi dake daukar Albashin dubu 60 zai auri mata 4 ya haifi ‘ya’ya 17 ace ba za’a samu matsala ba?

Yace gasunan a Abuja kullun suna ganinsu da robar bara idan ya gansu yakan yi tunanin shin nan gaba wane irin mutane wadannan yaran zasu zama?

Yace wasu zasu zargi Gwamnati amma maganar gaskiya wannan ba laifin Gwamnati bane.

Karanta Wannan  Venezuela ta zargi Amurka da sata da kuma fashin teku

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *