
Da alama dai Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ba zai samu damar halartar zaben fidda gwani na jam’iyyar ADC ba.
Saboda Mai shari’a Darius Khobo na babbar kotun jihar Kaduna ya sake daga sauraron belinsa sai satin farko na wajan Yuni.
ICPC na ci gaba da tsare malam Nasiru Ahmad El-Rufai inda ake zarginsa da almundahanar kudade da aikata ba daidai ba da mukamin da ya samu na Gwamna da sauransu.
Jam’iyyar ADC dai ta tsayar da karshen watan Afrilu zuwa Mayu dan gudanar da zaben fidda gwani.