
Babbar kotun tarayya dake Abuja ta daure tsohon Ministan wutar Lantarkin, Saleh Mamman bisa satar Naira Biliyan 33.8
A yau Alhamis ne kotun ta daureshi inda ta sameshi da aikata laifuka 12 wanda kotun tace bisa hujjojin da aka gabatar mata, ta gamsu cewa ya aikata laifukan.
Mai Shari’a, James Omotosho ne ya yanke wannan hukunci duk da cewa Saleh Mamman bai samu damar halartar wajan shari’ar ba.