
An ga Bidiyon kudi cike da jakar Ghana Must Go a Anbulan me dauke da suna da hoton shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ana rabawa mutane dan su sake zaben shugaban kasar.
Masu rabon kudin na sanye da riguna masu dauke da tamburan shugaba Tinubu kuma an jisu suna yarbanci.
Ko da a shekarar 2023 ma an ga irin wanan yanda aka rika rabawa mutane kudi a Ghana Must Go dan su zabi shugaban kasar.
A wancan lokacin har motar kudi irin ta banki aka ga ta shiga gidan na Tinubu dake Lagos.
A wasu rahotannin daga baya bayan ya ci zabe, sun ce shugaba Tinubu ya rika bayyana cewa kudinsa suka bashi damar zama shugaban kasa.