Sunday, May 17
Shadow

Da Duminsa: Na samu bayanai masu inganci cewa Gwamnati na shirin shyèkyè Malam Nasiru Ahmad El-Rufai>>Inji Timi Frank

Tsohon sakataren yada labarai na jam’iyyar APC, Timi Frank ya bayyana cewa, ya samu bayanai masu inganci dake tabbatar da cewa, Gwamnatin tarayya na shirin Shyèkyè malam Malam Nasiru Ahmad El-Rufai.

Ya bayyana cewa ya samu bayanan ne daga wata majiya ta tsaro.

Inda yayi zargin cewa, za’a sako Malam Nasiru Ahmad El-Rufai amma za’a bashi wani abu wanda bayan an sakeshi ba zai dade ba zai koma ga Allah.

Yace a tabbatar da lafiyar malam Nasiru Ahmad El-Rufai kuma duk abinda ya sameshi alhaki akan Gwamnati ne.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Musa Mai Sana'a ya kaiwa Hamza Al-Mustapha Ziyara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *