
Tauraron Tiktok, Usman A. Adams yayi ikirarin cewa, matsalar tsaron da ake kawowa daga jihar Zamfara karyace.
Yace Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya gama da duk wata matsalar tsaro.
Ya bayyana hakane a wani Bidiyo inda aka ganshi a wani daji da yace dajin jihar Zamfara ne kuma gashi ya je babu kowa a ciki.
Yace Bidiyon da ake yadawa a kafafen sada zumunta abubuwan dake faruwane a kasashen Sudan, Mali, da Somalia.