
Wata matashiya ta bayyana cewa, ta shiga motar haya tare da wani mutum da yayi ta fito da wayarsa ta iPhone 17 pro max yana nunawa.
Ta masa Bidiyo inda take dariya kan yanda yake nuna wayar tasa.
Wayar dai farashinta ya kai kusan Miliyan 4.
Da yawa na cewa ta yaya mutum zai fitar da wadannan kudin ya sayi waya amma bashi da motar hawa?