
Me martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya mayarwa da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima martani kan imaganar da yayi cewa, Dangote da BUA ba ‘yan Kano bane, ‘yan Lagos ne.
A cewar mataimakin shugaban kasar, Haihuwar Dangote da bUA kawai aka yi a Kano amma Lagos ce ta basu damar zama manyan masu kudin da suka zama.
Saidai a martanin Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II a wajan wani taro da aka gudanar kan kasuwanci a Kano.
Yace Dangote da BUA tun kamin su je Lagos dama can ‘yan kasuwane, sun fadada kasuwancinsu ne zuwa Lagos amma ba Lagos ce ta koya musu kasuwanci ba.
Dan haka ‘yan Kanone ba ‘yan Lagos.