
Dan kwallon Najeriya, dake buga wasa a kungiyar FK Vozdovac dake kasar Serbia ya rera wakar Fatima Bintu ta Nazifi Asnanic a tsakanin abokan kwallonsa.
An gansu suna masa tafi yayin da yake rera wakar.
Ya rera wakar ne yayin da suke a wajan cin abinci.
Da yawa sun jinjina masa saboda kishin yarensa da ya nuna.