Thursday, October 1
Shadow

An maka Dan Wike a gaban Kotu bisa zarcin cinye kudi dala Miliyan $2.1

Safwan Garba ya maka dan Ministan Abuja, Jordan Wike a Kotu kan cinye masa Kudi Dala Miliyan $2.1 watau kwatankwacin sama da Naira Biliyan biyu da dubu dari bakwai kenan 2.7Bn

Garba ya maka dan Ministan kara a gaban kotu inda yace sun hada kasuwanci dan gina Gidaje a Abuja.

Garba da yake gabatar da korafinsa a gaban Kotu yace a shekarar 2025 ne suka shirya shi da Dan Wike cewa shi dan Wike din zai kawo filaye a Abuja yayin da shi kuma zai kawo kudin da za’a gina filayen da suka kai dala Miliyan $4.2

Garba Yace dan Wike ya nuna masa wasu Filaye a Abuja yace anan ne zasu yi ginin gidajen inda yace zasu raba riba akan shi Garba ya rika karbar kaso 60 cikin 100 shi kuma dan Wike ya rika karbar Kaso 40 cikin 100.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Yanda wata Uwar Ango daga Arewa ta baiwa Amarya kyautar Fan Miliyan 10, kwatankwacin Naira Biliyan 25 kenan a matsayin Budan kai

Yace dan Wike ya rika baza masa wuta akan lalai ya bayar da kudin a fara aiki, inda yace ya tura masa lambar asusun bankinsa dan ya tura masa kudin.

Saidai dan Wike yace Tsabar kudin yake so watau Cash kuma a dalar Amirka yake sonsu ba a Naira ba.

Garba yace ya yadda suka hadu ya bayar da kudin a gaban wasu shaidu.

Yace kwanaki suka wuce amma shiru kake ji ba’a fara aiki a filayen ba yana ta zuwa zagaye.

Yace da ya kira dan Wike sai ya rika bashi Uzuri

Yace daga baya ma daina daukar wayarsa yayi.

Yace dan hakane ya nemi ganawa da babansa, Watau Ministan Abuja, Nyesom Wike.

Karanta Wannan  Hoto: An kama janar din soja inda aka kulleshi a Abuja saboda karkatar da shinkafar tallafi da sayar da motocin aiki da janare na ofishinsa

Yace ko da ya je gaban Wike ya kai masa korafi, sai Wike yace karya yake kuma shi dan damfara ne yasa ‘yansanda suka kamashi.

Yace a yanzu yana neman kotu ta kwato mai kudinsa da kuma dan Wike ya biyashi Naira Miliyan 100 kudin damuwar da ya sakashi ciki.

Dan Wike Jordan ya bayyana a gaban kotun inda tace ya bayar da fasfonsa na kasar Amurka.

Saidai Lauyansa, Ogwu Onu yayi rokon cewa kotun ta karbi kwafin Fasfon sai nan gaba idan ana bukatar na ainahin zai mikashi, kuma kotu ta amince da hakan.

Lauyan me Kara, Ibrahim Waru ya yiwa dan Wike Tambayoyi.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda aka ga Kwankwaso da Peter Obi na kuskus a wajan babban taron jam'iyyar su ta NDC

Ya Tambayeshi shin yasan da maganar kasuwancin?

Yace Eh.

Ya tambayeshi maganar kudi da aka bashi yace a’a.

Da ya nuna mai takarda da sa hannunsa yace bai san da itaba kuma sa hannun da aka gani a wajan na jabune ba nasa bane.

Lauyan ya tambayeshi shin ya kaiwa ‘yansanda korafi bayan ganin cewa an kwaikwayi sa hannunsa?

Yace a’a.

Kotu dai ta daga ci gaba da sauraren karar zuwa Ranar 1ga watan Disamba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *