
Babban malamin Addinin Islama Sheikh Lawal Triumph ya kalubalanci ‘yan Darika cewa, ina aka samu labarin cewa wai Sheikh Ibrahim Inyas ya dauki malamai daga Najeriya sun je ziyarar kabarin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam).
Wai da suka masa sallama sai ya amsa musu kuma ya kira sunan kowanne daga cikinsu, wannan yasa Larabawa mamaki suka yi ta shiga darika.
Yace yana son yasan a wace Jarida aka samo wannan labari sannan Fatima(AS) da Aliyu(AS) duk sun kaiwa Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ziyara kuma sun masa sallama amma bai kira sunayensu ba sai wadannan shehunnan?
Saidai an samu wani ya baiwa malam Amsa. Inda yacw shi yasan jaridar da aka samo wannan labarin.
Kalli Bidiyon sa a kasa: