‘Fiye da rabin albashina zai ƙare ne a kuɗin mota’
Masu ababen hawa sun ƙara kuɗin sufuri a Najeriya bayan ƙara kudin litar man fetur.
A ranar Talata ne Kamfanin Man fetur na Najeriya (NNPCL) ya yi ƙarin farashin man fetur, daga naira 617 zuwa 855, dangane da inda mutum ke zaune a ƙasar.
Sai dai duk da ƙarin farashin litar man fetur ɗin har yanzu ana ci gaba da fuskantar ƙarancinsa a yankunan ƙasar.
A Legas, birnin kasuwanci na ƙasar, ana samun dogayen layukan masu shiga mota kasancewar motocin safa ƙalilan ne ke lodi.
Paul Eniola Adewusi ta bayyana wa BBC cewa “yanzu na kashe naira 3,500 daga unguwar Victoria Island zuwa Mowe”.
Idenyi kuwa cewa ya yi “na biya kudin mota naira 2,000 daga Lakowe zuwa Victoria Island”.
Yayin da Mmrimara Ugo ta ce “asalin kudin mota da nake biya 800 ne, amma a jiya sai da na biya naira 1,900...