Bayan kammala ziyarar aikin da ya je yi kasar Ingila, Sarkin Ingila, King Charles ya yi bankwana da shugaba Tinubu da matarsa, Remi Tinubu.
https://twitter.com/i/status/2034590329593049506
Ana tsammanin nan ba da jimawa ba, shugaba Tinubu zai kamo hanyar dawowa gida Najeriya.
A yayin da ake ta cece-kuce kan cewa Idan mutum yayi Sallar Idi ba sai yayi ta Juma'a ba.
An samu karatun malamai dake tabbatar da hakan.
A jiya ne dai, Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa lallai ko da mutum yayi Sallar Idi, sai yayi Juma'a.
Malam yace idan za'a dauki daya a bar daya to mutum ya bar Idi yayi Juma'a.
Saidai Karatun malamai irin su Dr. Idris Dutsen Tanshi, da Sheikh Jafar Mahmoud Adam, da Sheikh Albani Zaria duk sun tafi akan cewa, idan mutum yayi Idi, ba lallai sai yayi Juma'a ko Azahar ba.
https://www.tiktok.com/@kggpetroleum245/video/7618656617374027029?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7618656617374027029&source=h5_m×tamp=1773920979&user_id=7483197776647635989&se...
Wannan Bidiyon wani bawan Allah ne masoyin Tauraruwar Tiktok, Babiana inda ya mata addu'a a dakin Ka'aba Allah ya bata nasara akan Sadiya Haruna.
https://www.tiktok.com/@amanar.gov.abbakabiryusu/video/7618880019942755604?_r=1&_t=ZS-94ojsC0fvjE&sp_source=7537614245375297080
A baya dai, Itama Sadiya Haruna ta je dakin ka'ba inda tace ta kai karan Babiana gaban Allah ya bi mata hakkinta.
Cece-kuce ya barke a kafafen sada zumunta bayan da Malamin Addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi yace aje Idi kuma aje Sallar Juma'a.
Malam yace idan ya zamana mutum daya zai je to ya je Juma'a ya bar Idi.
https://www.tiktok.com/@izzalatul.bidia/video/7618693269660175636?_r=1&_t=ZS-94oRqB9nibp&sp_source=7537614245375297080
Saidai bayan bayyanar wannan jawabi nasa, An rika yada tsohon Bidiyon Marigayi, Dr. Idris Dutsen Tanshi inda ya bayar da fatawar cewa idan mutum yayi Idi, ba lallai yayi Juma'a ko Azahar ba.
https://www.tiktok.com/@e.snig.ltd_tiga_01/video/7618735768973905173?_r=1&_t=ZS-94oSL7l8TdQ&sp_source=7537614245375297080
An hangi me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu tare da minista, Hannatu Musa Musawa akan keken Doki a kasar Ingila suna annashuwa.
Suna cikin tawagar shugaban kasa, Bola Ahmad da ta je kasar Ingila inda yake ziyarar aiki.
Wasu dai sun ce hakan bai dace ba lura da yanda Najeriya ke fama da matsalar tsaro.
https://www.tiktok.com/@arewacontinental/video/7618748690005511444?_r=1&_t=ZS-94oQdn8BA0H&sp_source=7537614245375297080
Sarkin Ingila, King Charles ya gayawa shugaba Tinubu, Naija No dey carry last.
Lamarin ya dauki hankula sosai inda akai ta tafi.
Wannan turancin 'yan Najeriya ne dake nufin ba'a barin Najeriya a baya.
Sarki Charles ya bayyana hakane a karshen jawabin da yayi a wajan taron cin abinci na girmamawa da aka shiryawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a Ingila.
https://twitter.com/i/status/2034390502196285860
Shugaba Tinubu dai na ziyarar aiki a Ingila irin ta ta farko da wani shugaban Najeriya yayi a cikin shekaru 37 da suka gabata.
Ana sa ran wannan ziyarar aiki zata jawo hankalin Ingila ta zuba jari a Najeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa, a yau, 30 ga watan Ramadana, ana ruwan sama a kasar Saudiyya.
An ga yanda ruwan ke sauka kuma mahajjata na cikin farin ciki.
Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami ma ya bayyana hakan inda yace Allah ya karba mana Ibadun mu.
https://twitter.com/i/status/2034495205965987962
Dan Najeriya, Faruk da ya je Nijar yace a kasar ta Nijar an ga watan Shawwal na sallah dan haka gobe za'a yi sallah.
Yace shima gobe zai ajiye Azuminsa yayi Sallah ba zai cika Azumi 30 ba kamar yanda za'a yi a Najeriya ba.
https://www.tiktok.com/@faruq_abuja_back_up/video/7618709603345288468?_r=1&_t=ZS-94nsQ1H1uz3&sp_source=7537614245375297080
Wannan wani Bahaushene dake aikin dansanda a kasar Saudiyya.
An ganshi yana gayawa wasu Alhazai Hausawa cewa idan suna bukatar taimako su masa magana.
https://www.tiktok.com/@ksa_6o/video/7618340843241344277?_r=1&_t=ZS-94nrUKzid28&sp_source=7537614245375297080
Da yawa sai sam barka suke masa.
Sarkin Ingila ya shiryawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu liyafar cin abinci ta musamman a ziyarar da ya kai kasar.
Shugaba Tinubu na ziyarar aiki a Landan inda yake neman kara karfafa alakar kasuwanci tsakanin Najeriya da Ingilar.
https://twitter.com/i/status/2034376430935523370