Matashiya Mary Habila shekararta 3 tana zaune a karkashina a gidan shakatawa ta watau Guest House>>Inji Ministan Ayyuka David Umahi
Ministan Ayyuka, David Umahi a karin farko yayi magana da 'yan jarida tun bayan rasuwar Mary Habila a gidansa.
Umahi Yace matashiyar ba mai aikin Tausa bace, kamar yanda aka rika yadawa, malamar Jinyace a Asibitin gwamnatin tarayya.
Yace kuma tana zaune a gidansa ne na shakatawa watau Guest House ita da wata, yace shskararta 3 a karkashinsa.
Yace kwana daya kamin rasuwarta, ta bayyanawa saurayinta cewa hancinta na zubar da Jyni.
Yace a ranar da zata rasu, sun yi waya da saurayinta da dare har tana ce masa bata so ya ajiye wayar amma ya ajiye, daga baya ya kirata, bata dauka ba.
Yace sai da aka balle dakin data rasu a ciki aka tarar da gawarta, sannan kuma an tarar da famfo na zuba, alamar tana shirin yin wanka ne.
Yace ya bayar da umarnin a yi bincike kan sanadin rasuwart...








