YANZU-YANZU: Atiku, Kwankwaso Da Peter Obi Sun Fara Tattaunawa Domin Hadewa Waje Daya Don Tunkarar Zaben 2027
Daga Comr Nura Siniya
Manya-manyan ‘yan adawa uku a Nijeriya da suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar, kwankwaso da Peter Obi na tattaunawa kan yiwuwar hadaka gabanin zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Mataimakin kakakin jam’iyyar PDP na kasa Ibrahim Abdullahi ne ya bayyana hakan a gidan talabijin na Channels a ranar Litinin.
Abdullahi ya ce, za su ajiye muradun kashin kansu a gefe su kulla kawance mai karfi don ceto Nijeriya a cikin kangin da jam’iyyar APC ta cefa kasar a shekarar 2027.
Ana dai ganin dunkulewar waje daya na da alaƙa da zaɓen shugaban kasa 2027 don kawar da gwamnatin APC kamar yadda masu sharhi suka bayyana.
Me za ku ce kan wannan yunkuri?