Saturday, December 13
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Bayan da mahaifin Bilyaminu ya fito ya ce ya yafewa Maryam Sanda kuma shine ma yayi kokarin ganin Shugaba Tinubu ya yafe mata, Wani dan Uwan Biliyaminun ya fito yace bayan rasuwar Biliyaminu, Mahaifin ya hanasu sakat akan Gado, Aka bashi Miliyan 5 amma yace bai yadda ba, ya je kotu saida aka bashi Miliyan 10 daga cikin kudin gadon

Duk Labarai
Bayan Fitowar mahaifin Bilyaminu, watau mijin Maryam Sanda wanda ta kashe yace ya yafewa Maryam Sanda, Asalima Shine ya shiga gaba wajan ganin shugaba Tinubu ya yafewa Maryam din. Wani dan uwan mamacin ya fito yace Malam Bello Halliru da aka kashe Bilyaminu ya rika damunsu kan maganar gado aka bashi Naira Miliyan 5, amma bai yadda ba, sai da ya kai kotu aka kara masa zuwa Naira Miliyan 10. Yace amma shine zai fito yana wannan magana. Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta. Yafewa Maryam Sanda da shugaba Tinubu yayi ya jawo cece-kuce sosai inda wasu ke ganin hakan bai kamata ba.
Kalli Bidiyon irin wulakancin da Sanatoci sukawa Sanata Natasha Akpoti a zauren majalisar da ya jawo cece-kuce da yiwa Sanatocin Allah wadai

Kalli Bidiyon irin wulakancin da Sanatoci sukawa Sanata Natasha Akpoti a zauren majalisar da ya jawo cece-kuce da yiwa Sanatocin Allah wadai

Duk Labarai
Sanata Natasha Akpoti ta tashi a zauren majaliar Dattijai inda ta kawo shawarar a yi kira ga hukumomin Immigration na Najeriya da su hada kai dana kasar Libya dan dawo da matan Najeriya da ke tsare a gidajen yarin kasar Libya. Sanata Natasha Akpoti ta yi zargin cewa, irin wadanan mata an yi safararsu ne kuma ana musu fyadde suna haihuwar yara a gidajen yarin. Dan hakane ta nemi a dawo da irin wadannan mata gida Najeriya. Saidai wannan kiran nata bai samu karbuwa ba. Inda sanatoci da yawa suka ki yadda su goyi bayanta. Sai daga karshe ne aka samu Sanata daya ya goyi bayanta. Lamarin dai ya jawo cece-kuce sosai inda aka rika sukar Sanatocin da nuna wariya ga Sanata Natasha a kuma nuna rashin kulawa ga 'yan Najeriya. https://twitter.com/PoliticsNGR/status/197821281280...
Dan takarar jam’iyyar Adawa na kasar Kamaru yace shine ya lashe zaben shugaban kasar

Dan takarar jam’iyyar Adawa na kasar Kamaru yace shine ya lashe zaben shugaban kasar

Duk Labarai
Jagoran adawar Kamaru Issa Tchiroma Bakary ya yi iƙirari samun nasara a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar ranar Lahadi. Cikin wani bidiyo da ya fitar, da tsakar daren da ya gabata, Mista Bakary ya gode wa al'ummar Kamaru kan ''yarda da samar da canji'' da ya ce sun yi a ƙasar. Iƙirarin nasa na zuwa a daidai lokacin da hukumar zaɓen ƙasar ke ci gaba da tattara sakamakon zaɓukan. “Ina son bayyanawa cikin girmamawa da nutsuwa cewa al'ummar Kamaru sun yi zaɓinsu, don haka ya kamata a martaba zaɓinsu,'' in ji Bakary. Ya kuma alƙawarta wallafa cikakken sakamakon zaɓukan daga rumfunan zaɓen ƙasar. “Haƙiƙa wannan nasara ba tawa kaɗai ba ce ni kaɗai, ta kowa ce,'' in ji shi. Kawo yanzu hukumomin Kamaru ba su ce komai ba game da iƙirarin jagorar adawar, to amma a baya ministan ci...
Gwamnan Jihar Edo, Okpebholo ya bayyanawa Kwamishinoninsa cewa, rashin saka hular Shugaba Tinubu zuwa wajan aiki babban laifi ne

Gwamnan Jihar Edo, Okpebholo ya bayyanawa Kwamishinoninsa cewa, rashin saka hular Shugaba Tinubu zuwa wajan aiki babban laifi ne

Duk Labarai
Gwamnan jihar Edo, Okpebholo ya bayyanawa ma'aikatan jiharsa cewa dolene duk wanda zai je wajan aiki ya zamana yana sa hular shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Yace rashin saka hular babban laifine wanda ba zai yafe ba. https://twitter.com/dammiedammie35/status/1978343107671273696?t=bC020eNHsq9RA8MLEvr4JA&s=19
Matashi me suna Abdullahi dan jihar Katsina da ya yi ridda ya koma Kirista ya fito ya godewa Allah inda yace da yana hanyar bata Amma yanzu Allah ya nuna masa hanyar gaskiya

Matashi me suna Abdullahi dan jihar Katsina da ya yi ridda ya koma Kirista ya fito ya godewa Allah inda yace da yana hanyar bata Amma yanzu Allah ya nuna masa hanyar gaskiya

Duk Labarai
Matashin nan na jihar Katsina wanda yayi ridda ya koma Kirista, ya fito ya kara tabbatarwa da mutane maganar komaw Kirista da yayi. Yace yana tuba ga Allah bisa kuskuren da yayi a baya na kasancewa a cikin addinin Musulunci. A yanzu yace ya kama Kiristanci wanda a tunaninsa shine daidai. https://www.tiktok.com/@mohammedmhammed76/video/7560690225362504968?_t=ZS-90YxF7JPKb2&_r=1
Kalli Bidiyo: Shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu yana tunanin kasar Faransa ce zata bashi mulki karo na 2 shiyasa yake musu biyayya>>Inji Shugaban Nijar

Kalli Bidiyo: Shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu yana tunanin kasar Faransa ce zata bashi mulki karo na 2 shiyasa yake musu biyayya>>Inji Shugaban Nijar

Duk Labarai
Shugaban mulkin soji na kasar Nijar, Tchani ya yi zargin cewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na Najeriya, yana tunanin kasar faransa ce zata bashi damar sake cin zabe a shekarar 2027. Yace dalili ma kenan da shugaba Tinubu kewa kasar ta Faranaa biyayya. Ya bayyana hakane a wara hira ta musamman da aa yi dashi inda ya bayyana irin gudummawar da kasar Nijar ta baiwa Najeriya a shekarun baya. https://www.tiktok.com/@habibou.adamou..227/video/7560880169209171212?_t=ZS-90XH5ls0HdB&_r=1
Kalli Bidiyon: Malmin Imamu Malik Dan Shi’ane sannan Turawan Ingila ne suka kawo Wahabiyanci dan raba kan Musulmai >>Inji Malam Nura Khalid

Kalli Bidiyon: Malmin Imamu Malik Dan Shi’ane sannan Turawan Ingila ne suka kawo Wahabiyanci dan raba kan Musulmai >>Inji Malam Nura Khalid

Duk Labarai
Malam Nura Kalid ya bayyana cewa da yawa basu sani ba, malamin Imamu Malik dan shine, yana daya daga cikin limaman Shi'a. Sannan yace Ita kuma Wahabiyanci, Turawan ne suka kawo ta fan raba kan musulmai. Ya bayyana hakane a wannan Bidiyon na kasa: https://www.tiktok.com/@digital_imaam/video/7560201522907319559?_t=ZS-90YJWxqxAxN&_r=1
Nine na roki Shugaba Tinubu ya yafe mata, saboda yanke mata hukunci ba zai dawo da dana ba>>Inji Mahaifin Mijin Maryam Sanda

Nine na roki Shugaba Tinubu ya yafe mata, saboda yanke mata hukunci ba zai dawo da dana ba>>Inji Mahaifin Mijin Maryam Sanda

Duk Labarai
Mahaifin mijin Maryam Sanda, Alhaji Ahmed Bello Isa ya bayyana cewa, shine ya roki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yafewa matar dansa duk da itace ta kashe dan nasa. Alhaji Ahmed Bello Isa yace aiwatarwa da Maryam Sanda hukuncin kisa ba zai dawo da dansa,Bilyaminu Bello ba. Yace maimakon haka ya zabi yafe mata dan a saketa ta kula da 'ya'yanta kanana. Ya bayyana hakane yayin ganawa da manema labarai a Abuja ranar Talata wadda suka gudanar shi da mahaifin Maryam Sanda, Alhaji Garba Sanda