Monday, December 22
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Lokacin da zan sauka daga Mulki, An so in dauko Nasiru El-Rufai a matsayin magajina, amma nace ban yadda ba sai ya Kara hankali tukuna>>Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo

Lokacin da zan sauka daga Mulki, An so in dauko Nasiru El-Rufai a matsayin magajina, amma nace ban yadda ba sai ya Kara hankali tukuna>>Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo

Duk Labarai
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, a lokacin da ya so sauka daga Mulki, an bashi shawarar ya dauko Malam Nasiru Ahmad El-Rufai a matsayin magajinsa. Yace amma a wancan lokacin yaki yadda da wannan shawarar. Yace dalili kuwa shine yace Sai El-Rufai ya kara hankali. Yace da wanda ya bashi shawarar ya ga irin ayyukan El-Rufai yake yi shine ya sake zuwa ya sameshi yace lallai ya yadda da maganarsa. El-Rufai dai yayi ministan Abuja a zamanin mulkin Tsohon shugaban kasar.
An kama wani dalibi a jihar Naija saboda zargin sukar Gwamnan Jihar

An kama wani dalibi a jihar Naija saboda zargin sukar Gwamnan Jihar

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Naija na cewa, an kama wani dalibin jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida University saboda zargin ya soki gwamnan jihar, Mohammed Umar Bago. Sunan dalibin da aka kama Abubakar Isah Mokwa kuma an kamashine ranar Alhamis a dakinsa dake garin Lapai. An kamashine bayan da yayi rubutu yana sukar Gwamnan Gwamnan a shafinsa na Facebook. Kakakin 'yansandan jihar, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar da kamen inda yace suna kan binciken wanda akw zargin.
Daga aika abokina ya gwada Budurwata yace yana sonta dan in gane ko da gaske tana sona, Yanzu in gajarce muku zance ya aureta>>Inji Usman Zannah

Daga aika abokina ya gwada Budurwata yace yana sonta dan in gane ko da gaske tana sona, Yanzu in gajarce muku zance ya aureta>>Inji Usman Zannah

Duk Labarai
Matashi Usman Zannah ya bayyana cewa, ya aika Abokinsa ya gwada budurwar sa yace yana sonta dan ya gane ko tana sonsa da gaske. Yace a karshe abokin nasa da Budurwar sun yi soyayyar gaske harma sun haihu. Lamarin Ya dauki hankulan Mutane sosai inda wasu suka rika jajanta masa, wasu kuma suka rika masa Allah kara.
Dalilin da ya sa na sauya hafsoshin tsaron Najeriya – Tinubu yayi karin bayani

Dalilin da ya sa na sauya hafsoshin tsaron Najeriya – Tinubu yayi karin bayani

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana dalilin da ya sa ya ɗauki matakain sauya hafsohin tsaron ƙasar, yana mai gode wa tsofaffin manyan jami'an tsaron da ya sauke. Wani saƙo da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta ya ce ya ɗauki matakin ne saboda "ƙyautata tsaron ƙasa" "Na amince da sauya shugabancin rundunar tsaro domin ƙarfafa tsarin tsaron Najeriya," in ji shi. "Ina gode wa Janar Christopher Musa da sauran hafsoshin tsaron da suka gabata saboda hidima da sadaukarwar da suka yi, kuma ina neman sababbin shugabannin da su kyautata ƙwarewar aiki, da ankararwa, da haɗin kai a tsakanin sojojinmu." Sauyin shugabannin rundunar sojin na zuwa ne a lokaci da ake ci gaba da raɗe-raɗi game da shirin juyin mulki da aka ce wasu sojoji sun tsara, zargin da rundunar sojin ta musanta. ...
Da Duminsa: Sati daya bayan rahotannin yunkurin jhuyin mulki Shugaba Tinubu ya kori manyan sojoji, Ya sauke Janar Christopher Musa daga shugaban sojoji, ya baiwa Gen. Olufemi Oluyede shugaban sojojin Najeriya

Shugaba Bola Tinubu ya tuɓe hafsan hafsoshin Najeriya, Janaral Christopher Musa da sauran hafsoshin tsaron ƙasar, a wani sauyi a tsarin jagorancin sojjin ƙasar domin inganta da ƙarfafa sha'anin tsaro a Najeriya. A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar mai sa hannun ɗaya daga cikin masu taimaka wa shugaban a harkar watsa labarai, Sunday Dare, Tinubu ya yi musu fatan alkairi tare da bayyana sunayen sabbin hafsoshin da za su maye gurbin waɗanda aka sauke ɗin. Jadawalin sabbin hafsoshin: Janar Olufemi Oluyede - Hafsan hafsoshi Manjo Janar W Sha'aibu - Hafsan sojojin ƙasa Air Vice Marshall S.K Aneke - Hafsan sojin sama Rear Admiral I. Abbas - Hafsan sojin ruwa Manjo Janar E.A.P Undiendeye - Shugaba sashen tattara bayan sirri na soji. Waɗanda suka tsira: Mal...
Jadawalin Sabbin Daraktocin Babban Bankin Najeriya ya nuna Yarbawa 10, Hausawa 3, Da Inyamurai 3 ne a cikinsa

Jadawalin Sabbin Daraktocin Babban Bankin Najeriya ya nuna Yarbawa 10, Hausawa 3, Da Inyamurai 3 ne a cikinsa

Duk Labarai
Wannan jadawalin sabbin Daraktocin babban bankin Najeriya, CBN ne dake ta yawo a kafafen sada zumunta. An ga Yarbawa 10, Hausawa 3 da Inyamurai 3 a ciki. Dr. Adetona Sikiru Adedeji - Director, Currency Operations and Branch Management. Dr. Olubukola Akinwunmi Akinniyi - Director, Banking Supervision. Yusuf Rakiya Opeyemi - Director, Payment System Supervision. Aisha Isa-Olatinwo - Director, Consumer Protection. Abdullahi Hamisu - Director, Banking Services. Dr. OJumu Adenike Olubunmi - Director, Medical Services. Mr. Makinde Kayode Olanrewaju - Director, Procurement & Support Services. Mrs. Jide-Samuel Omoyemen Avbasowamen - Director, Information Technology. Dr. Vincent Monsurat Modesola - Director, Strategy Management and Innovation. Mr. Solaja Mohamm...
Kalli Bidiyon: Shekaru 9 na kwashe ina son Aliko Dangote, har kamfaninsa na je amma ban samu damar ganinshi ba>>Inji Wannan matar

Kalli Bidiyon: Shekaru 9 na kwashe ina son Aliko Dangote, har kamfaninsa na je amma ban samu damar ganinshi ba>>Inji Wannan matar

Duk Labarai
Wannan matar ta bayyana cewa, Shekaru 9 ta kwashe tana son Aliko Dangote. Tace har kamfaninsa dake Obajana ta taba zuwa dan ta sanar dashi abinda ke zuciyarta amma bata samu damar ganinsa ba. Kalli Bidiyon hirar da aka yi da ita. https://www.tiktok.com/@dalafmkano/video/7564541578375646482?_t=ZS-90od3PbDnkH&_r=1
Inason gina Masallaci da kudaden da nike samu daga wakokin da nake yi, Kuma nasa ba zaku ce ba zaku yi Sallah a masallacin ba>>Inji Soja Boy

Inason gina Masallaci da kudaden da nike samu daga wakokin da nake yi, Kuma nasa ba zaku ce ba zaku yi Sallah a masallacin ba>>Inji Soja Boy

Duk Labarai
Tauraron mawakin batsa, Soja Boy me yawan jawo cece-kuce ya bayyana cewa burinsa shine ya gina Masallaci da kudin wakokin da yake yi. Yace yasa mutane ba zasu ki yin Sallah a masallacin da ya gina ba. Yace kuma zai gina makaranta shima yasan mutane ba zasu ce zasu ki yin karatu a makarantun da ya gina ba. https://www.tiktok.com/@_soulja.boy/video/7564135008919719189?_t=ZS-90ocRcpgd6H&_r=1
Kalli Bidiyo: Ban so Maiwushirya ya fasa auren ‘YarGuda ba, naso ya bari a daura auren, saboda damar mallakar gidace ta zo masa, Washe gari kawai ya fito yace ya saketa>>Inji Aminu J. Town

Kalli Bidiyo: Ban so Maiwushirya ya fasa auren ‘YarGuda ba, naso ya bari a daura auren, saboda damar mallakar gidace ta zo masa, Washe gari kawai ya fito yace ya saketa>>Inji Aminu J. Town

Duk Labarai
Tauraron Tiktok, Aminu J. Town ya bayyana cewa, ya raina rashin kunyar Idris Maiwushirya bayan da ya fito yace ya fasa auren 'yarGuda. J. Town yace So yayi Maiwushirya ya bari a daura auren, kwana daya kawai ya fito ya mata saki 3. https://www.tiktok.com/@aminujtown/video/7564522450814356744?_t=ZS-90obDB3RLjU&_r=1