Babban fasto a cocin The Methodist Church of Nigeria, Rev. Emmanuel Udofia ya bayyana cewa akwai yunwa a Najeriya.
Dalilin hakane ma yasa ya jawo hankalin fastoci 'yan uwansa dasu rika karfafa gwiwar mutane.
Ya kuma baiwa fastocin shawarar yiwa mutane addu'a da basu shawarwari masu kyau.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo Abuja daga kasar Saudiyya inda ya je wajan taron kasashen Musulmai.
Jirgin na shugaba Tinubu ya sauka ne da misalin karfe 8 na darennan a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe International airport.
Manyan jami'an gwamnati ne suka mai maraba bayan saukarsa.
Tabbas Kanunfari yana maganin sanyi kamar yanda masana ilimin kiwon lafiya suka tabbatar.
A mafi yawancin lokuta akan hada Kanunfari da zuma ne dan samun sakamakon maganin sanyi me kyau.
Masana sun bayyana hadin Kanunfari da zuma a matsayin na gaba-gaba wajan magance matsalar sanyi da mura.
A yayin da mutum ke fama da kaikayin makogoro, shima wannan hadi na da tasirin da zai magance wannan matsalar.
Yanda ake hadin shine:
Za'a samu Kanunfari kamar kwaya 6 a dan dorasu a wuta a dan gasa.
Sannan a daka su su zama gari.
Sai a zuba babban cokali na zuma a ciki.
Ana shan wannan hadi sau biyu zuwa uku a kullun dan maganin tari mura da kaikayin makogoro.
Kungiyoyin fafutuka 51 dake ikirarin yaki da rashawa da cin hanci sun nemi hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC ta kama shugaban jam'iyyar APC, Dr. Umar Abdullahi Ganduje kan zargin Rashawa da cin Hanci.
Kungiyoyin sun rubuta takardar neman a kama Gandujene ranar November 4, 2024 inda ita kuma hukumar EFCC ta karbi takardar ranar November 7, 2024.
A lokacin da yake rike da mukamin gwamnan Kano,an zargi Dr. Umar Abdullahi Ganduje da cin hanci da rashawa ta fannoni daban-daban.
Akwaidai shaidu 143 wadanda suke a shirye su bayar da shaida akan zargin cin hanci da rashawa na Ganduje wadanda suka hada da ma'aikatan kananan hukumomi da 'yan canji da tsaffin ma'aikatan banki.
Shuwagabannin kungiyoyin fafutukar da suka kai wadannan bukatu sun hada da Dr. Johnson Nebechi, Comrade...
Wannan wata mata ce da ta ke a kasar Amurka inda take aiki ana biyanta Naira Dubu 40 duk awa daya.
https://www.youtube.com/watch?v=9HFjRK5j9mo
Tace tana aiki ne a babban shagon sayayya na Amazon inda take aikin dare.
Da yawa dai sun bayyana sha'awar aikin nata.
Saidai wasu na ganin tsadar rayuwa da ake fama dashi a Amurka zai iya lakume kudaden da take samu.
Wannan Alh. Ibrahim Mijinyawa ne mamallakin manyan shagunan Sahad stores dake Kaduna, Kano,Abuja, Da Nasarawa.
Rahotanni sun ce bashi da girman kai sam kuma baya cin bashin banki sannan yana kyautatawa ma'aikatansa sosai.
Kuma yana kokarin fitar da Zakka.
Mutane 10 sun mutu da dama sun jikkata a wani mummunan hadarin mota da ya faru a jihar Jigawa.
Lamarin ya farune a karamar hukumar Taura dake jihar.
Wani Shaidar gani da ido ya gayawa manema labarai cewa hadarin ya farune a kauyen 'Yanfari dake kan hanyar Kano zuwa Hadejia a karamar hukumar Taura.
Yace motar bas ce ta daki wata Tirela dake a gefen titi inda motar ta wuntsula mutane 10 suka mutu nan take.
Kakakin 'yansandan jihar, DSP Lawan Shiisu ya tabbatar da faruwar lamarin.
Yace lamarin ya farune ranar November 12, 2024 kuma suna samun labari jami'an su suka garzaya wajan inda yace sun tarar direban motar da mutane 9 sun mutu.
Yace akwai mutum da ya da bai mutu ba a yanzu ana duba lafiyarsa.
Yace suna kan bincike dan gano ko akwai laifin wani a hadarin da ya faru.
Shugaban rukunin Kamfanin Mai Na NNPC, Mele Kyari ne ya bayyana nasarar kammala biyan bashin da ake bin kamfanin da ga kamfanonin mai na kasashen ƙetare inda ya ce a yanzu, babu mai bin kamfanin bashin sisin kwabo.Kyari ya ce, wannan babban nasara ce da aka cimma biyo bayan cire tallafin mai a Gwamnatin Shugaba Tinubu.
“Mun rika karkatar da kudadenmu da dukiyoyinmu don tabbatar da komai na tafiya daidai a bangaren mai na PMS mai wuyar sha'ani, abinda ya rika janye hankalin NNPC daga biyan basussuka"
Mele ya ci gaba da cewa“ Sai dai yanzu wannan matsala ta kau, za ku ga cewa ba mu da wani bashin da ake bin mu, kuma don mu tabbatar da dorewar hakan, ya zama wajibi a kawar da duk wata matsala don masana'antar ta iya samar da makamashi mai dorewa da arha da ake buƙata a ƙasar nan."
Sh...
Hukumar 'yansanda a Birnin Jos na jihar Filato ta tabbatar da fargabar dasa bam a birnin.
Saidai ta musanta wannan jita-jita.
Kakakin 'yansandan jihar, DSP Alfred Alabo ya tabbatarwa manema labarai cewa maganar dasa bam din ba gaskiya bane.
Yace ranar Talata ne aka fara yada jitajitar kuma jami'an su da suka kware wajan kula da bam sun isa wajan inda suka tabbatar da babu bam a inda ake rade-radin.
Infection na mata da suke fama dashi a gabansu abu ne wanda ya zama ruwan dare, a wani binciken masa na jami'ar Harvard sun bayyana cewa kaso 75 cikin 100 na mata sun taba samun ko kuma zasu samu cutar Infection a rayuwarsu.
Tafarnuwa na taimakawa sosai wajan magance matsalar cutar Infection tana hana abinda ke zama a farjin mace ya bata infection yaduwa.
Infection din gaban mata ana kiransa da Yeast infection a turance, shi Yeast din wani ruwa ne da a gaban kowace mace akwaishi, amma akan samu matsala wani lokacin sai yayi yawa sosai shine sai ya koma ya zama infection.
Ga alamomin da mace zata gane tana da cutar Infection kamar haka:
Idan kika ji gabanki na kaikai ko yana miki ba dadi.
Idan kina jin zafi yayin jima'i.
Idan farin ruwa me kauri na fita daga gabanki.
A...