Thursday, December 18
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Yayinnda manoma ke Korafi: Farashin kayan abinci ya sade faduwa kasa

Yayinnda manoma ke Korafi: Farashin kayan abinci ya sade faduwa kasa

Duk Labarai
Hukumar ƙididdiga ta Naajeriya, NBS, ta ce farashin kayayyaki ya faɗo karo na biyar a jere a ƙasar, a watan Agusta 2025, lamarin da ya kawo sauƙi ga mutanen ƙasar. Alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa, farashi ya sauko daga 21.88 a watan Yuli zuwa 20.12 a watan Agustan 2025. Abin da ke nuna cewa an samu raguwar kashi 1.76 cikin ɗari daga watan na Yuli zuwa Agusta. Hakan kuma na nufin farashin ya rikito idan aka kwatanta da 32.15 ciki ɗari da aka samu a watan Agustan 2024. Sai dai alƙaluman ba su yi wani tasiri na azo-a-gani ba a yankunan karkara, inda kuɗin mota da rarraba kayayyaki ke ci gaba da janyo tsadar kayayyaki fiye da a birane. Sai dai abinci, wanda shi ne ja gaba wurin kayayyakin da farashinsu ke ƙaruwa ya dawo matsakaici a watan na Agusta a ƙasar, ko da yake y...
Albashin da nake biyan Direbobin Tankana ya fi na wanda ya kammala jami’a>>Inji Dangote

Albashin da nake biyan Direbobin Tankana ya fi na wanda ya kammala jami’a>>Inji Dangote

Duk Labarai
Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa, Albashin da yake biyan direbobin Tankarsa ya fi na wanda ya kammala jami'a. Dangote ya bayyana hakane a wata ganawa da yayi da manema labarai inda yayi karin haske kan rikicinsa da Kungiyar NUPENG. Ya kuma gayyaci direbobin NUPENG duk wanda bai da aiki ya je zai bashi aikin tukin. Dangote yace Albashin Direban tankarsa ya nunka mafi karancin Albashin sau 4 wanda akalla zai kai sama da Naira dubu dari uku kenan.

DSS ta maka Sowore da X da Facebook a kotu saboda ya kira shugaba Tinubu me laifi kuma ya zargi shugaban kasar da fadar ba daidai ba game da magance matsalar rashawa da cin hanci a Najeriya

Duk Labarai
Hukumar 'yansandan farin kaya ta DSS ta maka mawallafin jaridar Sahara reporters, Omoyele Sowore a kotu bisa zarginsa da kiran shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu me laifi. Sannan an zargi Sowore da kuma bayyana shugaban kasar a matsayin makaryaci saboda yace yayi ikirarin magance matsalar rashawa da cin hanci a kasar Brazil amma Sowore yace maganar ba gaskiya bace. Sowore ya wallafa cewa DSS na shirin kaishi kotu kuma a shirye yake idan an kaishi Kotun ya ansa gayyata.
Babu Yunwa a Najeriya>>Inji Me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga

Babu Yunwa a Najeriya>>Inji Me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga

Duk Labarai
Me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya musanta ikirarin tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar cewa akwai yunwa a Najeriya. Atiku yace yunwar dake Najeriya da Talauci ka iya tunzura mutane su fita zanga-zanga irin wadda ake yi a kasashen Duniya. Saidai me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya musanta maganar ta Atiku inda yace Atiku be san halin da Najeriya take ciki ba a yanzu dan an kama hanyar ci gaba. Yace Hukumar kididdiga ta kasa, NBS ta fitar da bayanai cewa farashin kayan masarufi sun yi kasa, sannan a baya tace kudaden shigar Najeriya sun karu ta bangaren da ba na man fetur ba. Sannan yace Tinubu ya biya basuka da yawa da ake bin Najeriya. Yace kuma Tinubu ya dauki matakai na gyara kasa ba tare da tsoro ba.
Shugaba Tinubu ya yanke tudun da yake ba tare da ya kammala dan ya dawo gida Najeriya ya ci gaba da aiki>>Fadar Shugaban kasa

Shugaba Tinubu ya yanke tudun da yake ba tare da ya kammala dan ya dawo gida Najeriya ya ci gaba da aiki>>Fadar Shugaban kasa

Duk Labarai
Fadar Shugaban kasa ta sanar da cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yanke hutun da yake ba tare da kammalawa ba ya dan dawowa gida Najeriya. Me magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin. Yace shugaba Tinubu zai dawo gida Najeriya ranar Talata dan ci gaba da ayyukan raya kasa.
Gwamnati ta bayyana jihohi 11 da zasu fuskanci ambaliyar ruwa tsakanin nan da ranar Alhamis, Karanta ka ji ko jiharka na ciki

Gwamnati ta bayyana jihohi 11 da zasu fuskanci ambaliyar ruwa tsakanin nan da ranar Alhamis, Karanta ka ji ko jiharka na ciki

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta fitar da hasashe na jihohi 11 da ka iya fuskantar ambaliyar ruwa tsakanin ranar Lahadi da ranar Alhamis. Ma'aikatar Muhalli ta tarayya ce ta fitar da wannan sanarwar inda tace jihohin da lamarin zai shafa sun hada da: Adamawa State (Ganye, Natubi); Benue State (Abinsi, Agyo, Gogo, Ito, Makurdi, Udoma, Ukpiam); Nasarawa State (Agima, Rukubi, Odogbo); Taraba State (Beli, Serti, Donga); Delta State (Umugboma, Umukwata, Abraka, Aboh, Okpo-Krika); da Niger State (Rijau). Sauran Jihohin sune Kebbi State (Ribah); Kano State (Gwarzo, Karaye); Katsina State (Jibia); Sokoto State (Makira); da Zamfara State (Kaura Namoda, Shinkafi, Maradun, Gusau, Anka, Bungudu). Saidai mu yi fatan Allah ya tsare.