Tauraron fina-finan Hausa, Musa Mai Sana'a ya kaiwa Hamza Almustapha Ziyara inda yace ya kamata mutane su fahimci Najeriya ta hanyar matsawa kusa da manya.
https://www.tiktok.com/@maisanaakanotv/video/7569552251438632203?_t=ZS-91E93ODWmwr&_r=1
Rahotanni sun bayyana cewa, manyan sojojin Amurka sun fara baiwa shugaban kasar Amurka, Donald Trump shawara cewa ba lallai su yi nasara idan suka kawo Khari Najeriya ba.
Sojojin sun ce akwai yiyuwar za'a sake tafka kuskure irin wanda aka yi a kasashen Syria da Afghanistan da Libya.
Hakan na zuwane bayan da Sojojin suka mikawa shugaban kasar Amurkar tsarin kalar hare-haren da suke shirin kawowa Najeriya.
Wani dan Najeriya ya gargadi sojojin Amurka da cewa, Sauron Najeriya kadai ya ishi ya gama da Sojojinsu ida suka kawo mana Khari.
https://twitter.com/InibeheEffiong/status/1987065461067162097?t=1ClsUYiHCNjIEQloMqj_Iw&s=19
Wannan matashin Ya bayyana cewaz ya fi son Mawakin Siyasa Rarara da mahaifinsa.
Ya bayyana hakan a wani Bidiyon Tiktok da ya watsu sosai.
https://www.tiktok.com/@djaribaba5/video/7569844644968697095?_t=ZS-91DEPeBtAJM&_r=1
Malamin Addinin Islama ya bayyan cewa Darikar Tijjaniyya Kafurcice.
Malam ya bayyana hakane a wani Bidiyonsa da yake wa'azi inda yace ko mahaifinsa ne ya shiga Darikar Tijjaniyya to ya kafurta
Hakanan yace ko dansa ya shiga Darikar Tijjaniyya sai ya tsine masa ya koreshi daga gidansa
https://www.tiktok.com/@ibn.ali.alzakzaky/video/7570007527878937876?_t=ZS-91DCXAE1tgm&_r=1
Kasar Rasha a karin farko ta yi magana akan Barazanar harin da shugaban kasar Amurka, Donald Trump yace zai kawo Najeriya.
Kasar ta bakin me magana da yawun ma'aikatar harkokin kasashen waje, Maria Zakharova tace tana saka ido akan Najeriya da abinda ka iya faruwa
Ta yi kira ga kowane bangare dasu mutunta dokokin kasa da kasa.
Hakan na zuwa ne bayan da kasar China tace tana tare da Najeriya sannan bata goyon bayan kowace kasa ta kawowa Najeriya Khari.
Tauraron fina-finan Hausa, Musbahu Anfara ya bayyana rashin jin dadinsa kan yanda Hadiza Gabon ta yi Editing hirar da yayi da ita a shirin ta na Gabon Show.
Ya bayyana cewa bai ji dadin hakan ba.
Hakanan ya baiwa shuwagabannin gidan Solo Hakuri kan kalaman da yayi.
Saidai yace masu zaginsa su ci gaba dan yanzu a kafafen sada zumunta kowa ma zagi ake.
https://www.tiktok.com/@misbahu.aka.anfara/video/7569954858669821191?_t=ZS-91D8HvUZCOe&_r=1
Kundin bajinta na 'Guinness World Records' ya karrama matashiyar nan yar Najeriya Hilda Baci saboda girka dafa-dukar shinkafa mafi yawa a duniya.
A watan Satumban da ya gabata ne matashiyar ta yi wani gagarumin aikin girka dafa-dukar shinkafa mafi yawa cikin tukunya ɗaya a duniya.
Dafa-dukar shinkafa da ake yi wa laƙabi da 'jollof' abinci ne da ya shahara a ƙasashen Najeriya da Ghana da Senegal da Saliyo da Laberiya da ma wasu da dama.
Hilda mai shekara 28 a duniya ta yi shuhura ne a shekara ta 2023 bayan kafa tarihin kwashe lokaci mafi tsawo tana girki ita kaɗai, na tsawon sa'a 93 da minti 11
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi Sa'ad Abubaka III a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja yayin da barazanar Trump ta kai hari ƙasar ke ci gaba da jan hankali.
Ganawar tasu na zuwa ne bayan Tinubu ya gana da Archbishop na Abuja Ignatius Kaigama.
Fadar shugaban ba ta bayyana abin da suka tattauna ba, amma ana sa ran ba za ta wuce yunƙurin kwantar da hankali ba yayin da wasu ke yaɗa iƙirarin yi wa mabiya addinin Kirista kisan ƙare-dangi.
Daga baya sarkin ya bi sawun shugaban ƙasar wajen yin sallar Juma'a a fadar shugaban ƙasa
Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa, dolene Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya janye kalaman barazanar da yawa Najeriya sannan ya bayar da hakuri.
Ya bayyana hakane a wajan wani taron ganawa da matasa da yayi ranar Alhamis.
Sanata Barau yace Najeriya kasa ce me cin gashin kanta dan haka ba zata bari wata kasa ta zo tana mata barazana ko katsalandan ba.
Yace ko da abinda Trump yake fada gaskiyane ba sigar da ya kamata ya biyo ba kenan, kamata yayi majalisar Dinkin Duniya ce zata shiga tsakani saboda akwai dokar kasa da kasa.
yace mu ba dabbobi bane akwai dokokin da suka tanadi hanyoyin da ake bi dan daukar mataki akan matsaloli irin wannan ba wai barazana ba.