Da Duminsa: Ji Wata magana da Kwankwaso yayi da zata jawo a kamashi a Bincikeshi
Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar lauyoyin Najeriya, NBA sun ce zasu aikawa da hukumar 'yansandan Najeriya da sauran jami'an tsaro korafi dan a biciki tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kan wani ikirari da yayi.
Kungiyar ta bayyana hakane bayan zaman kwamitin zartarwasta, watau NEC
Sakataren kungiyar ta NBA, Etaba Agbor ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.
Maganar da ake zargin Kwankwaso da yi shine, yace a shakerar 2019 ya dauki Abba Kabir Yusuf zuwa ganin alkalan kotun koli ta Najeriya bayan da hukumar zabe me zaman kanta, INEC ta bayyana zaben Kano a matsayin Inconclusive, watau wanda bai kammalu ba.
A karshe dai kotun kolin ta tabbatarwa da Gwanduje a wancan lokacin cewa shine yaci zaben.
Wannan magana ta tayar da hankuka musamman tsakanin Lauyoyin Najeri...








