Sunday, December 21
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kamfanin mai na kasa, NNPCL ya sanar da kulle matatar man fetur ta Fatakwal

Kamfanin mai na kasa, NNPCL ya sanar da kulle matatar man fetur ta Fatakwal

Duk Labarai
Kamfanin man fetur na ƙasa NNPC ya sanar da rufe Matatar mai ta Fatakwal a hukumance. A wata sanarwa da ya fitar a Asabar din nan kamfanin na NNPC ya ce za a rufe matatar na tsawon wata ɗaya domin gudanar da wasu gyare gyare. A cewar babban jami’in sadarwa na kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, ya ce rufewar ta fara aiki ne daga yau Asabar 24 ga watan Mayu.
Kalli Bidiyo: Anata tsinewa wannan matar bayan da aka ga tana fada da tsohuwar da ta yi jika da ita tana dukanta

Kalli Bidiyo: Anata tsinewa wannan matar bayan da aka ga tana fada da tsohuwar da ta yi jika da ita tana dukanta

Duk Labarai
Wata mata ta sha tofin Allah tsine bayan da aka ga Bidiyon ta ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda take fada da tsohuwa wada zata iya yin jika da ita. https://twitter.com/BolanleCole/status/1926206225693213123?t=WlnHkQcRa1ONS13rPr1ifw&s=19 Badai a san a ina ne Lamarin ya faru ba amma an ga matar tana dukan tsohuwar da itace.
Kalli Yanda lamarin ya faru: ‘Yan tà’àddà sun nutse a ruwa yayin da suke gudun neman tsira an kàshè guda 21 yayin da sojoji suka kai musu samame a Katsina

Kalli Yanda lamarin ya faru: ‘Yan tà’àddà sun nutse a ruwa yayin da suke gudun neman tsira an kàshè guda 21 yayin da sojoji suka kai musu samame a Katsina

Duk Labarai
Sojojin Najeriya sun bayyana cewa, wasu 'yan ta'adda sun nutse inda suka kashe gudan 21 a samamen da suka kai musu a maboyarsu dake jihar Katsina. Lamarin ya farune ranar Juma'a, 23 ga watan Mayu na shekarar 2025. Lamarin ya farune a kauyen Ruwan Godiya, dake karamar hukumar Faskari ta jihar Katsinar. Hukumar sojin ce ta sanar da hakan ta shafinta na X inda tace rundunar sojojinta ta "Operation Fasan Yama," ce ta samu wannan nasarar.
Kasar Canada zata fara koro ‘yan Najeriya gida

Kasar Canada zata fara koro ‘yan Najeriya gida

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, kasar Canada na shirin tsaurara matakai na daukar 'yan kasashen waje aiki a kasar dake zuwa Cirani. Hakan na nufin 'yan kasashen waje da yawa dake aiki a kasar na fuskantar barazanar korarsu zuwa kasashen su, ciki hadda 'yan Najeriya. Kasar Canada din tace a yanzu kaso 10 cikin 100 ne kawai na ma'aikatan kamfanoni za'a rika barin ana daukar 'yan kasashen waje inda sauran 'yan asalin kasar Canada din za'a dauka. Dan hakane dole a yanzu kamfanonin kasar zasu rage ma'aikatansu wanda ba 'yan asalin kasar ba da maye 'yan asalin kasar.
Wike ya bayar da umarnin a kulle sakatariyar jam’iyyar PDP dake Abuja

Wike ya bayar da umarnin a kulle sakatariyar jam’iyyar PDP dake Abuja

Duk Labarai
Rahotanni dake fitowa daga babban birnin tarayya Abuja na cewa, Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayar da umarnin a kulle sakatariyar jam'iyyar PDP ranar Litinin. Ministan ya bayyana cewa za'a kulle sakatariyar ne tare da wasu gine-gine guda 4,793 da lasisin su ya kare kuma aka kwace. Hakan na zuwane a yayin da jam'iyyar ta PDP ke shirin babban taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ranar 27 ga watan Mayu. Tsama tsakanin Wike da jam'iyyar PDP ta barkene bayan da Wike yayi rashin nasara wajan samun tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar a shekarar 2023. Inda tun wancan lokaci ne ya kudiri aniyar yakar duk wani tsari na Atiku Abubakar.
Komowa jam’iyyar APC ba zai sa a dakatar da binciken da ake maka ba>>Gwamnatin Tarayya ta gayawa ‘yan siyasa

Komowa jam’iyyar APC ba zai sa a dakatar da binciken da ake maka ba>>Gwamnatin Tarayya ta gayawa ‘yan siyasa

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta gargadi 'yan siyasa masu tururuwar komawa jam'iyyar APC da cewa komawa jam'iyyar ba zai sa a dakatar da binciken da ake musu ba. Babban lauyan gwamnati, Prince Lateef Fagbemi, SAN ne ya bayyana haka ta bakin kakakinsa, Mr. Kamarudeen Ogundele inda yace Gwamnatin tarayya zata ci gaba da tabbatar da doka da oda. Yayi maganar ne bayan da me magana da yawun Atiku Abubakar yayi zargin cewa wasu manyan gwamnati sun gana da wani gwamnan jihar Kudu maso Kudu kamin ya koma APC. Fagbemi yace babu gaskiya a wannan ikirari inda yace yana kiran a yi watsi da maganar.
Jadawalin Manyan ‘yan bìndìgà shida da aka kàshè lokacin Tinubu

Jadawalin Manyan ‘yan bìndìgà shida da aka kàshè lokacin Tinubu

Duk Labarai
A daidai lokacin da ake fargabar mayar da hannun agogo baya a ƙoƙarin daƙile matsalar tsaro a arewacin Najeriya, wasu na ɗiga alamar tambaya kan me ya sa ake kwan-gaba-kwan-baya a yaƙin. A tsakanin watan Maris zuwa watan Afrilu, an fuskanci hare-hare a yankin arewa maso gabashin Najeriya, waɗanda ake zargin tsagin Boko Haram na ISWAP da kaiwa, ciki har da waɗanda suka kai sansanin sojoji. Wannan ya sa masana suke ganin lamarin na da ɗaga hankali musamman ganin ƴan ƙungiyar suna amfani da jirage marasa matuƙa, sannan suna amfani da nakiyoyi da suke birnewa a ƙasa. Haka kuma masana suna ganin raba hankalin sojojin da suke aikin yaƙi da matsalolin tsaro ya taimaka wajen kasa daƙile matsalar, domin an kwaso wasu manyan makamai da ma sojoji daga arewa maso gabas, aka mayar da su arewa ...
Salah ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Premier na bana

Salah ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Premier na bana

Duk Labarai
Ɗan wasan gaba na Liverpool Mohamed Salah ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Premier na kakar bana. Wannan ne karo na biyu da Salah ya lashe kyautar, wanda ake yi bayan haɗa kuri'un jama'a da na masana harkar kwallon kafa - ɗan wasan ya taɓa lashe kyautar a kakar 2017-2018. Salah wanda ya jagoranci ƙungiyarsa wajen lashe gasar Premier, ya doke abokan takararsa da suka haɗa da Virgil van Dijk da Ryan Gravenberch da kuma Declan Rice. Sauran waɗanda ya doke a lashe kyautar sun kunshi Alexander Isak da Bryan Mbeumo da kuma Chris Wood. Wannan ne karo na farko tun kakar 2018-2019 da ɗan wasan Manchester City bai lashe kyautar ba. Ɗan wasan ɗan asalin ƙasar Masar ya zura kwallaye 28 da kuma bayar da 18 aka ci a wannan kakar da ke daf da karewa.