Thursday, December 18
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Gobara ta tashi a makarantar Qur’ani ta Sheikh Dahiru Bauchi dake Rafin Albasa, Bauchi

Gobara ta tashi a makarantar Qur’ani ta Sheikh Dahiru Bauchi dake Rafin Albasa, Bauchi

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Bauchi na cewa, Gobara ta tashi a makarantar Sheikh Dahiru Usman Bauchi dake Rafin Albasa a jihar. Rahoton Daily Trust yace Gobarar ta cinye ginin wanda benene inda ta lalata kayan aiki dake ofis-ofis na cikin ginin. Zuwa yanzu dai ba'a gano dalilin faruwar Gobarar ba. Shugaban Gidauniyar Dahiru Bauchi, Sayyadi Aliyu Sise Dahiru ya jajantawa dalibai da malaman makarantar kan wannan ibtila'i. Yace sun godewa Allah da ba'a samu asarar rai ba. Yace Sheikh Dahiru Bauchi ne ya kafa makarantar inda Tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo ya budeta. Yacw an yi asarar litattafai na malam da na marigayi Sheikh Hadi Dahiru Bauchi, dana Ahmad Sheikh Dahiru da sauransu. Yace gobarar ta tashine bayan an tashi daga makarantar.
Hukumar tace finai finai ta jihar Kano ta dakatar da nuna fim din ‘Labarina’ da gidan Sarauta da wasu karin fina finai 20

Hukumar tace finai finai ta jihar Kano ta dakatar da nuna fim din ‘Labarina’ da gidan Sarauta da wasu karin fina finai 20

Duk Labarai
Hukumar tace finai finai ta jihar Kano ta dakatar da nuna fim din 'Labarina' da gidan Sarauta da wasu karin fina finai 20 A kokarinta na tabbatar da ana bin dokar tace fina-finai sauda kafa tare da kara dora masana'antar kannywood a kan saiti, Hukumar tace fina-finai da Dab'i ta Jahar Kano karkashin jagorancin Alh Abba El-mustapha ta dauki wani gagarun mataki domin tsaftace yadda ake sakin fina-finai barkatai batare da cika ka'idar da doka ta tanadar musu ba na kawo kowanne film gabanta a tantance shi kafin ya isa ga idanun al'umma inda ta dakatar da wasu Manyan Fina-finai har guda 22 daga sakasu a kafafen Internet ko gidan TV Abba El-mustapha ne ya bayyana wannan mataki biyo bayan tattaunawa da manyan jami'an Hukumar tare da dogon nazari domin kawo karshen korafe korafen da Hukumar ...
Sojin Nijeriya Sun Tàbbàtar Da Ķàšhè Babban Maķusàncin Bèllò Tùrjì A Yammacin Jiya, Lahadi

Sojin Nijeriya Sun Tàbbàtar Da Ķàšhè Babban Maķusàncin Bèllò Tùrjì A Yammacin Jiya, Lahadi

Duk Labarai
A wani gagarumin samame da suka gudanar, rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da samun nasarar hallaka babban makusancin shugaban 'yan Bîndîgâ, Bello Turji, wato Alhaji Shaudo Alku, a ranar 18 ga Mayu, 2025. Rahotanni sun bayyana cewa wannan artabu ya auku ne a kusa da makarantar Tunfa da ke ƙaramar hukumar Isa, Jihar Sokoto. Rundunar ta ce an kashe tare da su wasu daga cikin mabiyansu da dama, ciki har da masu hannu wajen kai hare-hare a sassa daban-daban na ƙasar nan. Wannan nasara na daga cikin kokarin da hukumomin tsaro ke ci gaba da yi don murkushe ayyukan ta’addanci da kuma dawo da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa. Allah ya kara tsare ƙasarmu da kuma bai wa jami’an tsaro nasara akan dukkan masu kawo fitina.
Ji yanda ta kaya tsakanin Shugaba Tinubu da Peter Obi a haduwar da suka yi a wajan rantsar da Paparoma

Ji yanda ta kaya tsakanin Shugaba Tinubu da Peter Obi a haduwar da suka yi a wajan rantsar da Paparoma

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour party, Peter Obi da tsohon Gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi sun hadu a fadar Vatican wajan rantsar da sabon Fafaroma Leo XIV. Kayode Fayemi ne yawa Peter Obi jagoranci zuwa wajan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu inda ya fara magana da cewa, Shugaban kasa barka da zuwa cocin mu, mun gode da ka amsa gayyatar Fafaroma. Tinubu ya amsa da cewa nine ya kamata ace na muku barka da zuwa. Yace nine shugaban tawagar Najeriya a wannan taron, sun amsa masa da cewa dukkansu suna karkashin Tawagarsa.
Yaro ya dauki Bìndìgàr mahaifinsu inda ya harbe kanwarsa ta mùtù

Yaro ya dauki Bìndìgàr mahaifinsu inda ya harbe kanwarsa ta mùtù

Duk Labarai
Karamin yaro dan shekaru 16 ya dauki Bindigar mahaifinsa ya harbe kanwarsa ta mutu har lahira a jihar Delta. Kakakin 'yansandan jihar, Bright Edafe ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace lamarin akwai sosa Zuciya. Ya kara da cewa, mahaifin yace shi mafarauci ne kuma dan nasa yakan rika wasa da Bindigar. Yace zuwa ya zu ba'a kai ga tantance sunayen wadanda lamarin ya faru dasu ba.
Ban ga wani abu da zai iya hana Tinubu zarcewa ba a 2027>>Tanko Yakasai

Ban ga wani abu da zai iya hana Tinubu zarcewa ba a 2027>>Tanko Yakasai

Duk Labarai
Dattijon Jihar Kano, Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana cewa a yanzu babu dan siyasar dake da karbuwa kamar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Ya bayyana hakane a ganawar da yayi da kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN inda yace Tinubu bai yi wa Arewa Laifin komai ba. Yace APC ce ke rike da mafi yawan jihohi kuna ko jihohin da jam'iyyar Adawa ke rike dasu duk sun nuna goyon bayan Tinubu dan haka bai ga me kada shi ba. Yace amma watakila abubuwa na iya canjawa inda yace amma maganar gaskiya a yanda ake tafiya bai ga wani abu da zai hana Tinubu zarcewa a shekarar 2027 ba.
An kama dattijo mai shekara 80 da miyagun ƙwàyòyì a Kaduna

An kama dattijo mai shekara 80 da miyagun ƙwàyòyì a Kaduna

Duk Labarai
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce jami'anta sun kama wani dattijo mai suna Ayuba Ashiru mai shekara 80 da kilo 2.3 na miyagun ƙwayoyi. A wata sanarwa da kakakin hukumar na ƙasa Femi Babafemi ya fitar wadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 14 ga Mayun 2025 a yankin Dogarawa da ke ƙaramar hukumar Sabon Garin jihar Kaduna ne bayan samun bayanan sirri a game da harƙallarsa. Sanarwar ta ce an taɓa kama Ashirun bisa fataucin miyagun ƙwayoyi, aka ɗaure na shekara goma tsakanin 2014 zuwa 2024. "Ya ce ya kasance a harƙallar fataucin miyagun ƙwayoyi na tsawon shekara 46," kamar yadda sanarwar ta nuna. Sanarwar ta kuma ƙara da cewa jami'an hukumar sun kama wata dattijuwa mai suna Uloma Uchechi Su...