Tuesday, December 16
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Bidiyo: Gafarar Allah da Rahamarsa ba wasa bane: Sai ka aikata zunubi yace a rubuta maka lada, ko ka aikata zunubu ya mantar da mala’ikun ba zasu rubuta ba>>Sheikh Maqari

Kalli Bidiyo: Gafarar Allah da Rahamarsa ba wasa bane: Sai ka aikata zunubi yace a rubuta maka lada, ko ka aikata zunubu ya mantar da mala’ikun ba zasu rubuta ba>>Sheikh Maqari

Duk Labarai
Babban malamin Addinin Islama Sheikh Ibrahim Maqari ya bayyana cewa, Rahamar Allah yawa gareta. Yace idan Allah yaso, sai mutum ya aikata Laifi a rubuta lada ko kuma ya aikata laifi a mantar da mala'ikun ba zasu rubuta zunubinba. Yace ko kuma idan mutum ya aikata Zunubi sai a aiko babbar gafara da zata shafe Zunubin da ya aikata. https://www.tiktok.com/@masoyinannabi509gmailcom/video/7502567487347739959?_t=ZM-8wF0fqcw2K7&_r=1 Da yawa sun yi Kabbarar Allahu Akbar.
Manyan Arewa kudi aka basu suka siyar daku shiyasa suke gayawa shugaban kasa, Arewa ba korafi, Subul da baka ne aka yi a Katsina maganar ta fito fili amma dama can haka suke gayawa shugaban kasa, saboda an biyasu, Inji Sheikh Nura Khalid

Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Nura Khalid wanda aka fi sani da Digital Imam ya bayyana cewa, Manyan Arewa kudi aka basu shiyasa basa iya fitowa su gayawa shugaban kasa gaskiya suke ce masa Arewa ba korafi. Kalmar Arewa ba Korafi ta fito ne daga jihar Katsina wadda ke fama da matsalar 'yan Bindiga a lokacin da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kai ziyara jihar, an ga wani babban allo dauke da kalmar Katsina ba Korafi. Lamarin ya jawo cece-kuce inda akai ta sukar musamman manyan masu mulki na Jihar, har sai da ta kai ga gwamnan jihar ya fito ya nesanta kansa da wannan allo. Saidai Sheikh Nura Khalid ya bayyana cewa, Subul da baka ne aa yi amma haka suke gayawa shugaban kasar.
Karanta Jadawalin mutane 9 da zasu yi takara da Sheikh Isa Ali Pantami wajan neman takarar Gwamnan jihar Gombe a shekarar 2027

Karanta Jadawalin mutane 9 da zasu yi takara da Sheikh Isa Ali Pantami wajan neman takarar Gwamnan jihar Gombe a shekarar 2027

Duk Labarai
Tuni dai magana ta yi karfi wajan bayyanar babban malamin Addinin Islama kuma dan siyasa, Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami wajan neman takarar gwamnan jihar Gombe a shekarar 2027. Sunayen sauran mutane 9 da zasu yi taka dashi sun bayyana kamar haka: Prof. Isa Ali Pantami Arc. Yunusa Yakubu Dr. Aminu Yuguda Muhammad Jibrin Barde Hon. Usman Bello Kumo Hon. Ali Isa JC Engr. Aliyu Mohammed (Kombat) Hon. Khamisu Ahmed Mailantarki Hon. Mohammed Gambo Magaji Barr. Sani Ahmed Haruna
Gwamna Abba Kabir Ya Bukaci A Kawo Masa Takardun Makarantar Tsohuwar Dalibar Jami’ar Da Ta Koma Sana’ar Wainar Fulawa Da Awara Saboda Rashin Aikin Yi

Gwamna Abba Kabir Ya Bukaci A Kawo Masa Takardun Makarantar Tsohuwar Dalibar Jami’ar Da Ta Koma Sana’ar Wainar Fulawa Da Awara Saboda Rashin Aikin Yi

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Gwamna Abba Kabir Ya Bukaci A Kawo Masa Takardun Makarantar Tsohuwar Dalibar Jami'ar Da Ta Koma Sana'ar Wainar Fulawa Da Awara Saboda Rashin Aikin Yi
Dangantaka ta yi tsami sosai tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da na Israela, Benjamin Netanyahu, shi kuma Trump baya son raini dan haka yace zai amince da kasar Falasdinawa ya ga tsiya

Rahotanni sun bayyana cewa, dangantaka ta yi tsami sosai tsakanin shugaban kasar Amurka Donald Trump da na Israela, Benjamin Netanyahu. Tun da farko dai hakan ya bayyana ne bayan da kasar Amurka ta amince ta taimakawa kasar Saudiyya mallakar tashar makamin Kare dagi, Nokiliya, ba tare da saka kasar Israela a cikin maganar ba. Kasar Israyla a baya itace take shigewa Amurka gaba akan kowane lamarin da ya shafi hulda da kasashen Gabas ta tsakiya, saidai a yanzu gashi an yi maganar makamashin nokiliya tsakanin Amurka da Saudiyya babu ita. Hakanan Amurka ta yi sulhu da mayakan kasar Yemen wanda shima ba'a saka kasar Israela cikin tattaunawar ba, a wasu rahotanni ma ance Amurkar bata ce kada mayakan Yemen su kaiwa kasar Israela hari ba a tattaunawar, ita dai kada a taba kadarorin ta. ...
Shugaba Tinubu yace ya matsawa yan Najeriya ne saboda komai ya daidaita, kuma talaka zai sha jar miya nan bada dadewa ba

Shugaba Tinubu yace ya matsawa yan Najeriya ne saboda komai ya daidaita, kuma talaka zai sha jar miya nan bada dadewa ba

Duk Labarai
Shugaba Tinubu yace ya matsawa yan Najeriya ne saboda komai ya daidaita, kuma talaka zai sha jar miya nan bada dadewa ba. Shugaba Tinubu yace tsare-tsaren sa na cire tallafin man fetur da sauransu da suka sa mutane cikin halin dauwa, nan gaba a'a ga amfaninsu. Shugaban yace tuni an fara ganin Amfanin wadannan tsare-tsaren saboda farashin kayan Masarufi sun fara sauka. Tun bayan da shugaba Tinubu ya cire tallafin man fetur ne dai aka shiga tsadar rayuwa a Najeriya wadda har yanzu ba'a dawo daidai ba.
YANZU YANZUHukumar EFCC zata binciki ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, akan zargin wawure Naira biliyan 528

YANZU YANZUHukumar EFCC zata binciki ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, akan zargin wawure Naira biliyan 528

Duk Labarai
EFCC Ta Yi Alkawarin Bincikar Matawalle akan zargin wawure sama da Naira biliyan 528. Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta yi alkawarin gudanar da bincike kan zargin karkatar da kudi da aka yi wa Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, biyo bayan wani koke da jam’iyyar All Progressives Congress Young Leaders Alliance (APC-YLA) ta gabatar. Zarge-zargen dai na zargin Matawalle da wawure sama da Naira biliyan 528 a lokacin da yake Gwamnan Jihar Zamfara. Wannan tabbacin ya zo ne a wata zanga-zangar da aka gudanar ranar Juma’a a hedikwatar EFCC da ke Abuja, inda shugaban jam’iyyar APC-YLA Convener, Mohammed Ireji, da sauran masu zanga-zangar suka bukaci a sake bude shari’ar cin hanci da rashawa da ake yi wa Matawalle. Ireji ya nuna shakku kan jinkirin...
Duk da doka ta bukaci hakan, Ma’aikatan Gwamnatin ciki hadda shugaban kasa, Tinubu, Kashim, da Akpabio sun ki bayyana kadarorin da suka mallaka, kuma an kasa hukuntasu

Duk da doka ta bukaci hakan, Ma’aikatan Gwamnatin ciki hadda shugaban kasa, Tinubu, Kashim, da Akpabio sun ki bayyana kadarorin da suka mallaka, kuma an kasa hukuntasu

Duk Labarai
Dokar da'ar Ma'aikatan gwamnatin Najeriya, CCB ta bukaci dukun wani ne rike da mukamin siyasa ko masu hidima masa su bayyana kadarorin da suka mallaka kamin su hau mulki da kamin su saka. Dokar kuma ta tanadi cewa dole su bayyana kadarorin da matansu ko mazansu idan macece suka mallaka da wanda 'ya'yansu wanda basu yi aure ba suka mallaka. Saidai da yawa basa bin wannan doka kuma an kasa hukuntasu. Cikin wadanda basu bi wannan doka ba hadda shuwagabannin Najeriya, watau Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima da kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio. Hakan na zuwane duk da kiraye-kirayen kungiyoyin fafutuka na neman su bayyana kadarorin nasu. Ookar dai ta tanadi bayyana kadarorin ne dan tsaftace aikin gwamnati da satar dukiyar Talaka da kuma hana ra...
Da Duminsa: Gwamnonin Arewa zasu Gana a Kaduna game da matsalar tsaron da ta addabi yankin

Da Duminsa: Gwamnonin Arewa zasu Gana a Kaduna game da matsalar tsaron da ta addabi yankin

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnonin Arewacin Najeriya zasu gana a Kaduna saboda tattaunawa matsalar tsaro da ta addabi yankin. Rahoton yace hadimin gwamnan jihar Gombe, Ismaila Misilli ne ya bayyanawa manema labarai na Punchng hakan inda yace gwamnan Gomben shine ya kira wannan taron a matsayinsa na shugaban Gwamnonin Arewan. Yace idan dai ba an canja ba, a yau, Asabar ne za'a yi wannan taro a Kaduna kuma matsalar tsaron yankin ce babban abinda za'a tattauna.