Saturday, December 20
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Ƴan Majalisar Wakilai 6 daga jihar Delta sun fice daga PDP zuwa APC

Ƴan Majalisar Wakilai 6 daga jihar Delta sun fice daga PDP zuwa APC

Duk Labarai
Ƴan Majalisar Wakilai 6 daga jihar Delta sun fice daga PDP zuwa APC Ƴan majalisar wakilai 6 daga jihar Delta sun sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC. Shugaban majalisar, Abbas Tajuddeen ne ya bayyana haka a zaman majalisar na yau Talata bayan ta dawo daga hutu. Yan majalisa shidan da su ka sauya sheka daga PDP zuwa APC sun hada da Victor Nwokolo; Dan majalisa Julius Pondi; Dan majalisa Thomas Ereyitomi; Nicholas Mutu; Okodiko Jonathan da kuma Nnamdi Ezechi. Wasu ‘yan jam’iyyar Labour ma guda biyu daga jihar Enugu su ma sun sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa ta PDP, waɗanda su ka hada da Mark Obetta da Dennis Nnamdi. Shugaban majalisar ya ambato ‘yan majalisar na cewa sun sauya sheka ne sakamakon rikicin da ya barke a jam’iyyunsu a jihohinsu da kuma a matakin ...
Nnàmdì Kanu ya karyata lauyan da ke kare shi ana tsaka da zaman kotu

Nnàmdì Kanu ya karyata lauyan da ke kare shi ana tsaka da zaman kotu

Duk Labarai
Nnamdi Kanu ya karyata lauyan da ke kare shi ana tsaka da zaman kotu An samu ɗambarwa a kotu ranar Talata yayin da shugaban haramtacciyar ƙungiyar, IPOB , Mazi Nnamdi Kanu, ya karyata wani lauya mai suna Charles Ude da ya bayyana kansa a matsayin wanda ke wakiltarsa. Kanu yana fuskantar tuhume-tuhume da suka shafi ta’addanci a gaban kotu. A lokacin zaman kotun, alkalin da ke jagorantar shari’ar ya jawo hankalin ɓangarorin da ke cikin shari’ar zuwa wata wasika daga Charles Ude, wanda ya ce shi ne lauya na gaskiya da ke kare wanda ake tuhuma. Sai dai tawagar lauyoyin da ke kare Kanu sun ce ba su san Ude ba, kuma Kanu da kansa ya tabbatar da hakan, yana mai jaddada cewa Agabi ne kawai lauyansa. Kotu ta kuma tabo batun yawan lauyoyin da ke wakiltar wanda ake tuhuma. A cew...
HOTO: Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya gana da shugaban ƙasa Bola Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ranar Litinin.

HOTO: Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya gana da shugaban ƙasa Bola Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ranar Litinin.

Duk Labarai
HOTO: Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya gana da shugaban ƙasa Bola Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ranar Litinin. Wannan dai ita ce ziyarar aiki ta farko da ya kai wa shugaban ƙasar biyo bayan sauya sheka da ya yi zuwa jam’iyyar (APC). Gwamna Oborevwori ya isa gidan gwamnatin da misalin karfe 3:30 na rana. kuma manyan jami'ai ne suka tarbe su kafin su tafi ganawar sirri da shugaban.
Iyalan Mafarautan Da Aka Kàshè A Edo Sun Yi Zanga-zangar Neman Diyya

Iyalan Mafarautan Da Aka Kàshè A Edo Sun Yi Zanga-zangar Neman Diyya

Duk Labarai
Iyalan Mafarautan Da Aka Kashe A Edo Sun Yi Zanga-zangar Neman Diyya. Iyalan wasu mafarauta da suka rasa rayukansu a harin da ya faru a jihar Edo sun gudanar da zanga-zanga domin neman a biya su diyyar ‘yan uwansu da kuma gurfanar da wadanda suka aikata wannan mummunan laifi. Zanga-zangar, wadda ta gudana kwanaki 40 bayan aukuwar lamarin, ta samu halartar daruruwan ‘yan uwa da abokan arziki na wadanda abin ya shafa, wadanda suka fito dauke da takardu da hotunan wadanda suka mutu suna rokon gwamnati da hukumomin tsaro su dauki matakin gaggawa. Wani daga cikin shugabannin iyalan, ya bayyana cewa:"Har yanzu ba a kama ko daya daga cikin wadanda suka aikata wannan kisa ba. Mun gaji da jiran shiru. Muna so a tabbatar mana da adalci kuma a tallafa mana da diyya domin wadanda suka bar...
Ministan ilimi a Najeriya, Tunji Alausa ya ce hana satar amsa ne ya janyo faɗuwar ɗalibai a jarawabar shiga manyan makarantu da JAMB ke shiryawa a kowace shekara

Ministan ilimi a Najeriya, Tunji Alausa ya ce hana satar amsa ne ya janyo faɗuwar ɗalibai a jarawabar shiga manyan makarantu da JAMB ke shiryawa a kowace shekara

Duk Labarai
Ministan ilimi a Najeriya, Tunji Alausa ya ce hana satar amsa ne ya janyo faɗuwar ɗalibai a jarawabar shiga manyan makarantu da JAMB ke shiryawa a kowace shekara. Ya ce sakamakon zaɓen bana da aka samu, ya nuna irin yadda aka ƙara inganta yanayin rubuta jarabawar yadda ya kamata. Tunji ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da gidan talabijin na Channels a Najeriya ranar Talata, inda ya ce hakan kuma ya nuna yadda tsarin rubuta jarabawar ya daƙile satar amsa da ɗalibai ke yi. Alausa ya ƙara da cewa kada a ɗauki akamakon zaɓen na JAMB a matsayin koma-baya, maimakon haka a kalle shi a matsayin yadda ɗaliban da suka ci suka nuna hazaƙa lokacin rubuta jarabawar. "JAMB na gudanar da jarabwarta ta hanyar amfani da tsarin kwamfuta wato CBT. Sun ɗauki ƙwararan matakai da ya janyo aka ...
Majalisar Dattawan Najeriya ta kafa kwamitin kula da mulkin jihar Ribas

Majalisar Dattawan Najeriya ta kafa kwamitin kula da mulkin jihar Ribas

Duk Labarai
Majalisar Dattawan Najeriya ta kafa kwamiti mai mambobi 18 domin sanya idanu kan yadda gwamnan riƙo na jihar Ribas Vice Admiral Ibok Ete Ibas mai ritaya ke tafi da aikinsa. Majalisar ta ce ta ɗauki matakin ne a wani yuƙuri na ƙarfafa shugabanci na gari ba tare da rufa-rufa ba a jihar da ke kudu maso kudancin Najeriya. Shugaban Majalsiar Dattawa Godswill Akpabio ya sanar yayin zaman majalisar na yau Talata cewa kafa kwamitin na da matuƙar mahimmancin wajen sa ido kan abubuwan da ke faruwa a jihar. Shugaban masu rinjaye Opeyemi Bamidele ne shugaban kwamatin, mambobin kuma sun haɗa da Adamu Aliero, da Osita Izunaso, da Osita Ngwu, da Kaka Shehu, da Aminu Abass, da Tokunbo Abiru, Adeniyi Adebire. A watan Maris ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Ribas sakamakon a...
‘Yànbìndìgà sun dame mu a Shanono da Bagwai, in ji ɗanmajalisar Kano

‘Yànbìndìgà sun dame mu a Shanono da Bagwai, in ji ɗanmajalisar Kano

Duk Labarai
Danmajalisar da wakiltar mazaɓar Ɓagwai da Shanono a Majalsar Wakilan Najeriya ya nemi ƙarin jami'an tsaro sakamakon abin da ya kira hare-haren 'yanfashin daji a yankin. Yusuf Badau ya yi kiran ne yayin wani ƙudiri da ya gabatar a gaban zauren majalisar yau Talata, inda ya lissafa lokutan da aka kai musu wasu hare-haren. "Yan bindigar sun fara kai hari ne wata kasuwa da ke garin Farin Ruwa a ƙaramar hukumar Shanono ranar 17 ga watan Afrilu, inda suka kashe mutum biyu, da raunata mutum shida kuma suka sace mutum ɗaya," in ji shi. "Sun sake kai irin wannan hari a garin Shanono ranar 26 ga watan Afrilun, sai dai mutanen garin sun tari ƴanbindigar kuma suka kore su. "A ranar 2 ga watan Mayu a garin Fafarawa da Sandamu na Shanono da Bagwai, sun yi garkuwa da mutum daya da sace wayoy...