Wednesday, January 14
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Tawagar ‘yan Kwallon Najeriya ta Super Eagles ne kadai basu je da masu goyon bayansu gasar cin kofin Africa ta AFCON ba a hukumance

Tawagar ‘yan Kwallon Najeriya ta Super Eagles ne kadai basu je da masu goyon bayansu gasar cin kofin Africa ta AFCON ba a hukumance

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Tawagar 'yan kwallon Najeriya ne kadai basu je gasar cin kofin AFCON dake wakana yanzu haka ba a kasar Morocco da tawagar masu goyon bayansu ba a hukumance. Rahotanni sun ce hukumomin kwallon kafar Najeriya sun ki zuwa da tawagar masu goyon bayan da aka saba zuwa dasu ne saboda wai babu kudi.
Kalli Bidiyon: Yanda wani dan siyasa ya sha da kyar a hannun Talakawa a jihar Kaduna

Kalli Bidiyon: Yanda wani dan siyasa ya sha da kyar a hannun Talakawa a jihar Kaduna

Duk Labarai
Wani dan siyasa ya sha da kyar a hannun Talakawa a jihar Kaduna. A Bidiyon da aka ga yana ta yawo a kafafen sadarwa, an ga mutane ma ta jifarsa suna fadar cewa bama yi. https://twitter.com/ADCVanguard_/status/2004159712368251018?t=QM4sH0Ih2PxAaO7ahRwQ5A&s=19 A makon da ya gabata dai Hutudole ya kawo muku Rahoton yanda kusan irin haka ta faru a jihar Zamfara inda acan ma wani dan siyasa ne ya sha da kyar.
Wani Bidiyo da aka dauka na fadar shugaban kasa dake Abuja ta sama ya tona Asirin gidan, da yawa na cewa bai kamata a bari Bidiyon ya hau kafafen sada zumunta ba

Wani Bidiyo da aka dauka na fadar shugaban kasa dake Abuja ta sama ya tona Asirin gidan, da yawa na cewa bai kamata a bari Bidiyon ya hau kafafen sada zumunta ba

Duk Labarai
Wani Bidiyo da aka dauka na fadar shugaban kasa, Villa, ya dauki hankula. Bidiyon an daukeshi ne da jirgi marar Matuki ta sama wanda ya nuna kowane sashe na fadar shugaban kasar dake Abuja. Bidiyon ya yadu sosai a kafafen sada zumunta inda aka ga mutane na ta Allah wadai da fadar cewa bai kamata a bari wani ya dauki irin wannan Bidiyon ya yadashi a kafafen sada zumunta ba. Wasu na kafa Misalai da cewa, a kasashen Duniya da suka ci gaba har ma dana Afrika ba za'a bari irin haka ta faru ba. https://twitter.com/afrisagacity/status/2004089422380159165?t=U9mRlPprOZ06tlFgWuiuKQ&s=19
Kalli Bidiyon: Ni ina tare da A’isha Buhari game da abinda ta fada akan Buhari duka gaskiya ne>>Inji Matashi Sarkin Yakin Sunnah

Kalli Bidiyon: Ni ina tare da A’isha Buhari game da abinda ta fada akan Buhari duka gaskiya ne>>Inji Matashi Sarkin Yakin Sunnah

Duk Labarai
Matashi me sunan Sarkin Yakin Sunnah yace yana tare da duk abinda A'isha Buhari ta fada akan Marigayi, Muhammadu Buhari inda yace tafi kowa kusa dashi. Yace masu zaginta duk tafi su son Buhari kuma gaskiya ta fada a Littafin. Yace shin so suke ta yi masa karyane? https://www.tiktok.com/@umarpitykhalid0/video/7587422723895381268?_t=ZS-92Vp9fvRmrZ&_r=1
Kalli Bidiyon: Shugaban kasar Israyla, Benjamin Netanyahu ya bayar da umarnin a gaggauta daina abinda akewa Kiristoci a Najeriya

Kalli Bidiyon: Shugaban kasar Israyla, Benjamin Netanyahu ya bayar da umarnin a gaggauta daina abinda akewa Kiristoci a Najeriya

Duk Labarai
Shugaban Israyla, Benjamin Netanyahu a sakon da ya fitar na Kirsimeti, ya nemi a gaggauta daina yiwa Kiristoci muzancin da ake musu a Duniya. Bidiyon kalaman nasa sun dauki hankula a kafafen sada zumunta. Wasu Kiristoci sun bayyana jin dadi sosai da wannan sakon nashi. https://twitter.com/Harmless12345/status/2003953061715468505?t=98A_qhTVu5Un83uAw3FVIw&s=19
Malaman Jinya 16,000 ne suka tsere daga Najeriya zuwa kasar Ingila

Malaman Jinya 16,000 ne suka tsere daga Najeriya zuwa kasar Ingila

Duk Labarai
Rahotanni sun ce malaman jinya 16,000 ne wanda suka yi karatu a Najeriya suka tsere zuwa kasar Ingila suke aiki a can. Hakan ya farune a tsakanin shekarun 2017 zuwa 2025. Kuma Rahoton yace hadda Ungozoma ne ke tserewa daga Najeriyar zuwa kasar Ingila. An samu wannan bayanai ne daga rijistar da kasar Ingilar ta fitar. Wannan na nuni da cewa, Najeriya na fuskantar karancin malaman jinya yayin da 'yan kasar ke tserewa zuwa kasashen Turai dan aiki a can saboda albashi me kyau da ake biya acan din.