Wednesday, January 14
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Gidan Talabijin din Channels TV na shan suka saboda yanda suka kawo Rahoton abinda ya faru a masallaci jiya a jihar Borno

Gidan Talabijin din Channels TV na shan suka saboda yanda suka kawo Rahoton abinda ya faru a masallaci jiya a jihar Borno

Duk Labarai
Kafar Channels TV suna shan suka saboda yanda suka rubuta Rahoton abinda ya faru a masallaci a jihar Borno jiya. Abin fashewa ya fashe a masalacin jihar Borno inda wasu suka rasa rayukansu, wasu kuma suka jikkata. Saidai Channels TV a rahoton data kawo tace abin fashewar ya fashene a Maiduguri yayin da ake bikin Kirsimeti. Da yawa dai sun zargi Channels TV da Munafurci saboda bas saka cewa a masallaci abinnya faru ba hakanan wasu na cewa babu abinda ya hada tashin abin fashewar da Kirsimeti tunda ba a coci ya faru ba. https://twitter.com/abdool_moh/status/2003928512697127192?t=dGCUI_2x8o4uCjHm8S_MRw&s=19
Hattara: Musulmai da yawa na cin Alade ba tare da sun sani ba, inji Malam Triumph

Hattara: Musulmai da yawa na cin Alade ba tare da sun sani ba, inji Malam Triumph

Duk Labarai
Malam Lawal Triumph ya bayyana cewa, ya ji wani malami na wa'azin cewa akwai wani abu da ake sayarwa wanda da Alade ake yinsa kuma mutanen mu musulmai na ci. Yace amma malamin bai fito da abin fili ba watakila saboda yana tsoron kada kamfanin su kaishi kara ne. Malam yace tun da dai ba da sanin mutane ke ci ba, basu da laifi. https://www.tiktok.com/@taskarmalanlawantriumph/video/7587549699377302804?_t=ZS-92VaLuRO7iS&_r=1
Dr. Ahmad Gumi ya maka wasu masu Amfani da facèbòòk a kotu bisa zargin bata masa suna

Dr. Ahmad Gumi ya maka wasu masu Amfani da facèbòòk a kotu bisa zargin bata masa suna

Duk Labarai
Malamin addinin Islama, Dr. Ahmad Gumi ya maka wasu mutane 2 a kotu saboda zargin bata masa suna. Malam ya shigar da karanne ta hannun lauyansa, Suleiman Danlami Lere, Esq., kuma wadanda ake Tuhuna sune George Udom da- Bello Isiaka. Ana zarginsu da yada wani rubutu da suka dangantashi da Sheikh Gumi inda suka ce wai yawa sabon Ministan tsaron, Christopher Musa barazanar cewa wai idan bai daina kaiwa Tshàgyèràn Dhàjì hare-hare ba, zai kaiwa iyalansa hari. Sheikh Gumi yace wannan rubutu karyane kuma bashi yayi shi ba. https://twitter.com/el_uthmaan/status/2003886918912651402?t=Ktz8lxPRke7IGbeFjVhmyQ&s=19

Na yi Azumi na roki Allah a daga ranar Tashin Qiyama kuma ya amince, Inji Fasto Ebo Noah wanda ya cewa mabiyansa ranar Kirsimeti za’a yi tashin Qiyama

Duk Labarai
Faston nan dan kasar Ghana da yayi ikirarin an masa wahayi wai ranar Kirsimeti za'a yi tashin Qiyama, yanzu kuma ya fito yace ya roki Allah a daga ranar tashin qiyar kuma an daga. Yace dalili shine yana son ya fadada jiragen ruwan da ya gina da zasu dauki mutane dan kamar a cewarsa ruwane za'a yi wanda zai mamaye Duniya. Faston dai yayi kira ga mabiyansa dasu tuba. https://twitter.com/withAlvin__/status/2003920200392134840?t=qkAwSQeruSOEOlUWqh4T4g&s=19