Sunday, March 29
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Wike ya bayar da umarnin a kulle sakatariyar jam’iyyar PDP dake Abuja

Wike ya bayar da umarnin a kulle sakatariyar jam’iyyar PDP dake Abuja

Duk Labarai
Rahotanni dake fitowa daga babban birnin tarayya Abuja na cewa, Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayar da umarnin a kulle sakatariyar jam'iyyar PDP ranar Litinin. Ministan ya bayyana cewa za'a kulle sakatariyar ne tare da wasu gine-gine guda 4,793 da lasisin su ya kare kuma aka kwace. Hakan na zuwane a yayin da jam'iyyar ta PDP ke shirin babban taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ranar 27 ga watan Mayu. Tsama tsakanin Wike da jam'iyyar PDP ta barkene bayan da Wike yayi rashin nasara wajan samun tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar a shekarar 2023. Inda tun wancan lokaci ne ya kudiri aniyar yakar duk wani tsari na Atiku Abubakar.
Komowa jam’iyyar APC ba zai sa a dakatar da binciken da ake maka ba>>Gwamnatin Tarayya ta gayawa ‘yan siyasa

Komowa jam’iyyar APC ba zai sa a dakatar da binciken da ake maka ba>>Gwamnatin Tarayya ta gayawa ‘yan siyasa

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta gargadi 'yan siyasa masu tururuwar komawa jam'iyyar APC da cewa komawa jam'iyyar ba zai sa a dakatar da binciken da ake musu ba. Babban lauyan gwamnati, Prince Lateef Fagbemi, SAN ne ya bayyana haka ta bakin kakakinsa, Mr. Kamarudeen Ogundele inda yace Gwamnatin tarayya zata ci gaba da tabbatar da doka da oda. Yayi maganar ne bayan da me magana da yawun Atiku Abubakar yayi zargin cewa wasu manyan gwamnati sun gana da wani gwamnan jihar Kudu maso Kudu kamin ya koma APC. Fagbemi yace babu gaskiya a wannan ikirari inda yace yana kiran a yi watsi da maganar.
Jadawalin Manyan ‘yan bìndìgà shida da aka kàshè lokacin Tinubu

Jadawalin Manyan ‘yan bìndìgà shida da aka kàshè lokacin Tinubu

Duk Labarai
A daidai lokacin da ake fargabar mayar da hannun agogo baya a ƙoƙarin daƙile matsalar tsaro a arewacin Najeriya, wasu na ɗiga alamar tambaya kan me ya sa ake kwan-gaba-kwan-baya a yaƙin. A tsakanin watan Maris zuwa watan Afrilu, an fuskanci hare-hare a yankin arewa maso gabashin Najeriya, waɗanda ake zargin tsagin Boko Haram na ISWAP da kaiwa, ciki har da waɗanda suka kai sansanin sojoji. Wannan ya sa masana suke ganin lamarin na da ɗaga hankali musamman ganin ƴan ƙungiyar suna amfani da jirage marasa matuƙa, sannan suna amfani da nakiyoyi da suke birnewa a ƙasa. Haka kuma masana suna ganin raba hankalin sojojin da suke aikin yaƙi da matsalolin tsaro ya taimaka wajen kasa daƙile matsalar, domin an kwaso wasu manyan makamai da ma sojoji daga arewa maso gabas, aka mayar da su arewa ...
Salah ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Premier na bana

Salah ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Premier na bana

Duk Labarai
Ɗan wasan gaba na Liverpool Mohamed Salah ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Premier na kakar bana. Wannan ne karo na biyu da Salah ya lashe kyautar, wanda ake yi bayan haɗa kuri'un jama'a da na masana harkar kwallon kafa - ɗan wasan ya taɓa lashe kyautar a kakar 2017-2018. Salah wanda ya jagoranci ƙungiyarsa wajen lashe gasar Premier, ya doke abokan takararsa da suka haɗa da Virgil van Dijk da Ryan Gravenberch da kuma Declan Rice. Sauran waɗanda ya doke a lashe kyautar sun kunshi Alexander Isak da Bryan Mbeumo da kuma Chris Wood. Wannan ne karo na farko tun kakar 2018-2019 da ɗan wasan Manchester City bai lashe kyautar ba. Ɗan wasan ɗan asalin ƙasar Masar ya zura kwallaye 28 da kuma bayar da 18 aka ci a wannan kakar da ke daf da karewa.
Masu karamin karfi zamu sayarwa gidaje 753 da muka kwace daga hannun Emefiele a farashi me sauki>>Gwamnatin Tarayya

Masu karamin karfi zamu sayarwa gidaje 753 da muka kwace daga hannun Emefiele a farashi me sauki>>Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, masu karamin karfi ne zasu sayarwa da gidaje 753 data kwace daga hannun tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele. Hukumar EFCC ta bayyana cewa wannan gidaje shine kadara guda daya mafi girma da suka taba kwacewa a hannun barawon Gwamnati. Tuni dai hukumar ta EFCC ta mika wadannan gidaje ga ma'aikatar kula da gidaje da ci gaban birane ta tarayya.
Magidanci ya kàshè Kaninsa saboda ya mari matarsa

Magidanci ya kàshè Kaninsa saboda ya mari matarsa

Duk Labarai
Kwamishinan 'yansanda na jihar Delta, CP Olufemi Abaniwonda ya tabbatar da cewa wani mutum me suna Paul ya cakawa kaninsa wuka ya mutu har lahira saboda ya mari matarsa. Lamarin ya farune a Ugbokodo, dake karamar hukumar Okpe. Shima kakakin 'yansandan jihar, SP Bright Edafe ya tabbatar da faruwar lamarin. Yace kudin matar yayan nasa ne suka bace Naira Dubu biyu wanda ta zargeshi da dauka shi kuma yace bashi ya dauka ba. Saidai ita ta nace cewa shi ya dauka inda har ta cukumeshi anan ne mahawara ta yi zafi inda ya falla mata mari. Nan ta tafi ta kira mijinta ta gaya masa, shi kuma ba tare da bincike ba ya dauki daya daga cikin 'ya'yansa suka bi kanin nasa suka dakeshi da caka masa wuka har ya mutu. Jama'ar unguwar sun kona gidan mutumin da shagon matarsa inda saida 'yansa...
An kama matar da ake zargi da kashe jinjirin kishiyarta da guba

An kama matar da ake zargi da kashe jinjirin kishiyarta da guba

Duk Labarai
Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta ce ta kama da tsare wata mata mai suna Zaliha Shu'aibu bisa zargin kashe ɗan kishiyarta ɗan wata uku da haihuwa da maganin ƙwari. A wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar ta Kaduna, DSP Mansur Hassan ya fitar, al'amarin ya faru ne a ranar 13 ga watan nan na Mayu a gidansu da ke ƙauyen Malari a ƙaramar hukumar Soba. Sanarwar ta ce shaidu sun ce uwar yaron dai ta fita daga ɗakinta domin shiga banɗaki lokacin da kishiyar tata ta shigar mata ɗaki kuma bayan ta koma ɗakin ne ta ga kishiryar rungume da ɗan nata. Bayan ta miƙa mata jaririn ne sai uwar ɗan ta fahimci yadda kumfa ke fita daga bakin yaron nata sannan kuma akwai rauni a wuyansa, inda yaron ya kece da kuka. Bayan bincike, rundunar ƴansandan ta ce matar ta tabbatar da cewa ta aik...
A yayin da Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ke cewa zai kayar da Tinubu a 2027, dansa Bello El-Rufai yace Tinubu ne zabinsa a 2027

A yayin da Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ke cewa zai kayar da Tinubu a 2027, dansa Bello El-Rufai yace Tinubu ne zabinsa a 2027

Duk Labarai
Dan tsohon Gwamnan Kaduna, Bello El-Rufai ya bayyana goyon bayansa ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben 2027. Hakan na zuwane yayin da mahaifinsa, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ke jam'iyyar SDP da kuma shan Alwashin sai ya kayar da Tinubu daga kan Mulki. Bello Wanda dan majalisar wakilai ne me wakiltar Kaduna ta kudu, na daga cikin wanda suka halarci babban taron jam'iyyar APC inda jam'iyyar ta bayyana shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a matsayin dan takararta na shekarar 2027. A watan Maris da ya gabata ne dai El-Rufai ya bayyana cewa ya fice daga jam'iyyar APC saboda a cewarsa ta bar turbar da aka kafata akai. Reno Omokri da yake mayar da martani kan lamarin yace idan har El-Rufai ba zai iya jawi hankalin dansa ya bar Tinubu ba ta yaya zai iya jawo hankalin 'yan Najeriy...