Saturday, March 28
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Majalisar tarayya za ta yi bincike kan matsalolin da aka samu a JAMB ta bana

Majalisar tarayya za ta yi bincike kan matsalolin da aka samu a JAMB ta bana

Duk Labarai
Majalisar tarayya za ta yi bincike kan matsalolin da aka samu a JAMB ta bana Majalisar Wakilai ta yanke shawarar gudanar da bincike kan kuskuren fasaha da ya shafi sakamakon Jarrabawar UTME na shekarar 2025. Majalisar ta amince da wannan kuduri ne a zaman ta na ranar Alhamis, bayan ta amince da kudurin gaggawa mai muhimmancin jama’a da dan majalisa daga jihar Osun, Adewale Adebayo, ya gabatar.
Muzanta Naira: Kotu ta yanke wa wani dan Tiktok hukunci a Kaduna

Muzanta Naira: Kotu ta yanke wa wani dan Tiktok hukunci a Kaduna

Duk Labarai
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC reshen Kaduna ta samu nasara bayan da kotu ta yanke hukunci ga wani a mai amfani da shafukan Tiktok da Instagram, Muhammad Kabir. An gurfanar da wanda ake zargin ne a gaban Mai Shari’a R.M. Aikawa na Babban Kotun Tarayya dake zamanta a Kaduna, bisa laifin wulakanta kudin Naira. Shugaban sashen hulda da jama’a na EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana cewa an kama Kabir ne a ranar Talata, 29 ga Afrilu, 2025 a Tudun Wada, jihar Kaduna, bayan ya wallafa wani bidiyo a shafukansa na Tiktok da Instagram (@youngcee0066), yana watsar da takardun kudi na Naira a ƙasa, yana taka su da kafa, tare da furta wasu kalmomi cikin harshen Hausa yana kalubalantar EFCC da ta zo ta kama shi a inda aka san yana zaune. An kama shi bisa karya dokar Babban Bankin Najer...
Majalisar wakilai na son a maida yin zaɓe ya zama wajibi ga ƴan Nijeriya

Majalisar wakilai na son a maida yin zaɓe ya zama wajibi ga ƴan Nijeriya

Duk Labarai
Majalisar wakilai na son a maida yin zaɓe ya zama wajibi ga ƴan Nijeriya Wani ƙudiri da ke neman maida yin zaɓe ya zama wajibi ga ƴan Nijeriya ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai. Ƙudurin, wanda shugaban majalisar, Tajuddeen Abbas ya ɗauki nauyi, ya tsallake karatu na biyu bayan an yi wata zazzafar muhawara a zauren majalisar a yau Alhamis.
An samu Ci Gaba: Gwamnatin Najeria ta bayyana cewa za ta ƙaddamar da tauraron ɗan’adam guda huɗu da za su taimaka wajen lura da yanayin ƙasa da kuma yaƙi da matsalolin tsaro da ake fama da su

Gwamnatin Najeria ta bayyana cewa za ta ƙaddamar da tauraron ɗan'adam guda huɗu da za su taimaka wajen lura da yanayin ƙasa da kuma yaƙi da matsalolin tsaro da ake fama da su. Wadannan taurarin dan'adam ɗin za a yi amfani da su wajen nazarin dazuka da kai kawon jama’a da kuma wadda za ta ɗauko hotunan tekuna da tsaunuka da kuma gano sauran ma’adinai. Ministan sadarwa da fasahar zamani na ƙasar Uche Nnaji ne ya bayyana hakan a lokacin wani taron majalisar zartaswa ta ƙasa da ya shafi kirkira da fasahohin zamani karo na ashirin da biyu, wanda ya gudana a babban birnin ƙasar Abuja. Gwamnatin dai ta ce za ta ƙaddamar da waɗannan taurarin ɗan'adam ne domin gudanar da muhimman ayyukan da suka shafi saka ido a kan yankuna da wuraren da ke fama da matsalar tsaro da kuma ɗaukar muhimman ho...
Ba AI bane: Kalli hotunan Yanda aka ga wani abu me kama da surar mutum a sararin samaniyar kasar Greece, saidai masana Kimiyya sunce kada wanda ya tayar da hankalinsa, Tauraron dan Adam ne ya hasko Duniya

An ga wadannan hotunan a sararin samaniyar kasar Greece. Da farko idan mutum ya kalla, zai yi tsammanin AI ne, amma kafofin yada labarai da yawa irin su Beauty of Planet Earth dake wallafa labarai da hotunan ababen kayatarwa a Duniya sun tabbatar da faruwar lamarin. Saidai masana kimiyya sunce wannan ba wani abin tashin Hankalo bane, tana iya yiyuwar tauraron dan Adam ne rana ta haskashi shine hasken ya hasko cikin Duniya. lamarin ya farune ranar 14 ga watan Mayu.
Saikace ba kasar Larabawa ya je ba: Kalli Bidiyon yanda matan larabawa suka tarbi shugaban kasar Amurka Donald Trump da shigar banza, babu Hijabi ba dan kwali a kansu da ya jawo cece-kuce

Saikace ba kasar Larabawa ya je ba: Kalli Bidiyon yanda matan larabawa suka tarbi shugaban kasar Amurka Donald Trump da shigar banza, babu Hijabi ba dan kwali a kansu da ya jawo cece-kuce

Duk Labarai
Bidiyon matan Larabawa babu Hijabi babu dankwali akansu ya jawo cece-kuce sosai a yayin da aka gansu suna tarbar shugaban kasar Amurka, Donald Trump a kasar UAE. Matan dai dake da dogayen Gashi sun rika wasa da gashin a gaban Shugaba Trump. https://twitter.com/MargoMartin47/status/1922995639455044017?t=PJ0FlItXLf_841VVjSttDg&s=19 Lamarin ya bayar da mamaki kasancewar kasar Musulunci ce ya je kuma kasar Larabawa.
Farashin kayan masarufi sun yi sauki a Najeriya

Farashin kayan masarufi sun yi sauki a Najeriya

Duk Labarai
An samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya daga kashi 24.23 a watan Maris ɗin 2025 zuwa kashi 23.71 a watan Afrilun 2025. Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya, NBS ta ce hauhawar farashin da aka samu a watan Afriliu ya nuna an samu ragin kaso 0.52 na hauhawar idan aka kwatanta da watan Maris. “Wannan na nuni da cewa hauhawar farashin Ta shekara-shekara Ta ragu a watan Afrilun 2025 idan aka kwatanta da watan Afrilun 2024." Dangane kuma da hauhawar farashin kayan abinci a watan Afrilun 2025 ta kasance kaso 21.26 kamar yadda ke faruwa a shekara-shekara.
KARON FARKO: Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, ya ziyarci Babban Masallacin Sheikh Zayyad da ke Abu Dhabi, wanda ke ɗaya daga cikin manyan masallatai a duniya mai cike da fasahar gini ta zamani

KARON FARKO: Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, ya ziyarci Babban Masallacin Sheikh Zayyad da ke Abu Dhabi, wanda ke ɗaya daga cikin manyan masallatai a duniya mai cike da fasahar gini ta zamani. Trump ya ziyarci masallacin ne a yayin ziyararsa zuwa babban birnin Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE). Ya samu rakiyar Sheikh Khaled bin Mohamed, Yarima Mai Jiran Gado na Abu Dhabi.