Ministan ilimi a Najeriya, Tunji Alausa ya ce hana satar amsa ne ya janyo faɗuwar ɗalibai a jarawabar shiga manyan makarantu da JAMB ke shiryawa a kowace shekara
Ministan ilimi a Najeriya, Tunji Alausa ya ce hana satar amsa ne ya janyo faɗuwar ɗalibai a jarawabar shiga manyan makarantu da JAMB ke shiryawa a kowace shekara.
Ya ce sakamakon zaɓen bana da aka samu, ya nuna irin yadda aka ƙara inganta yanayin rubuta jarabawar yadda ya kamata.
Tunji ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da gidan talabijin na Channels a Najeriya ranar Talata, inda ya ce hakan kuma ya nuna yadda tsarin rubuta jarabawar ya daƙile satar amsa da ɗalibai ke yi.
Alausa ya ƙara da cewa kada a ɗauki akamakon zaɓen na JAMB a matsayin koma-baya, maimakon haka a kalle shi a matsayin yadda ɗaliban da suka ci suka nuna hazaƙa lokacin rubuta jarabawar.
"JAMB na gudanar da jarabwarta ta hanyar amfani da tsarin kwamfuta wato CBT. Sun ɗauki ƙwararan matakai da ya janyo aka ...








