APC ta zargi Gwamnatin Kano da ciyo bashin Dala Miliyan 6.6 daga ƙasar waje tare da neman bahasin yadda aka yi da kuɗaɗen
Wata ƙungiya a cikin jam’iyyar APC a jihar Kano mai suna APC Patriotic Volunteers ta zargi gwamnatin jihar da karɓar bashi daga ƙasashen waje har Dala Miliyan 6.6 ba tare da bayyana inda kuɗaɗen suka tafi ba.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Usman Alhaji ne ya yi wannan zargi a taron manema labarai da aka gudanar a Kano a yau Laraba.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa taron manema labaran an shirya shi ne domin nazarin ayyukan gwamnatin jam’iyyar NNPP a Kano cikin shekaru biyun da ta yi a kan mulki.
A cewar Alhaji Usman, ƙungiyar na da hujjoji daga Ofishin Kula da Lamuran Bashi na Ƙasa (DMO) da ke nuna cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta karɓi bas...
Kungiyar yarbawa magoya bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu me suna (NOYAT) sun yiwa shugaban kasar Alkawarin samar masa da kuri'u Miliyan 10.
Kungiyar a shekara 2022 ta shirya taro na musaman kan goyon bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a jihar Kaduna wanda ya samu halartar manyan mutane ciki hadda malaman addini.
A sanarwar da kungiyar ta fitar ranar Laraba, ta sanar da cewa, tana jinjinawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu saboda nada Yazeed Shehu Danfulani shugaban hukumar inshora ta manoma ta kasa, (NAIC).
Kungiyar a sanarwar wadda kakakinta, Mr. Seun Ogunyinka ya ftar tace nadin ya karfafa matasa sannan kuma 'yan Najeriya da dama sun ji dadi inda suka bayyana Danfulani a matsayin gwarzo wanda aka sanshi da aiki Tukuru.
Kasar Amurka ta bayar da umarnin kwashe ma'aikatan ta dake ofishin jakadancinta na kasar Iraqi inda ta bayyana cewa akwai fargabar tsaro.
Hakanan rahotanni sun ce Amurkar ta na kwashe wakilanta daga kasar UAE
Ana tsammanin haka shirine na Afkawa kasar Ìràn da yaki saboda hanata mallakar makamin kare dangi.
Kasar Iran tace muddin Amurka ko Israyla suka kai mata hari, zata tabbatar ta kaiwa kadarorin kasar Amurkar dake yankin Gabas ta tsakiya hari.
Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, ba zasu bar Iran ta mallaki makamin kare dangi ba.
Rahotanni sun ce kasar Iran ta ki baiwa Amurka hadin kai a tattaunawar neman sulhu dan karta mallaki makamin kare dangi.
Rahotanni sunce akwai artabu da dauki ba dadi da akw tsammanin zau faru a yau tsaanin masu zanga-zanga da jami'an tsaro a majalisar tarayya dake Abuja.
Masu zanga-zangar ta ranar 'yanci shin shirya zanga-zangar a Abuja dama gurare 19 a fadin kasarnan.
A yau ne ake sa ran shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai halarci majalisar tarayya dan karrama wasu 'yan majalisar sannan a canne zai gabatarwa da 'yan kasa jawabi.
A baya dai, shugaban kasar ya so ya gabatar da jawabin ga 'yan kasa da safiyar Ranar Alhamis amma daga baya aka canja tsari aka ce sai ya je majalisar tarayya.
Maau zanga-zangar sun ce zasu gabatar da kokensu ne game da matsalar matsim tattalin arzikin da talakawa ke ciki.
Tun daga 29 ga watan Mayu na shekarar 2023 bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya zama shugaban Najeriya, an sakawa manyan gurare na gwamnati guda 7 sunansa.
Daga cikin abubuwan da aka sakawa sunan Shugaban kasar akwai tituna, Barikin sojoji, dakunan taro da sauransu.
Wata kungiyar rajin kare hakkin bil'adama me suna (NEFGAD) ta bayyana hakan a matsayin abinda bai dace ba dan ya sabawa aikin gwamnati.
Ga jadawalin gurare 7 da aka sakawa sunan shugaban kasar kamar haka:
Babban Filin Jirgin sama na jihar Naija.
A ranar March 10, 2024 ne gwamnan jihar Naija, Umar Bago ya sakawa babban filin sauka da tashin jiragen jihar dake Minna sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Titun Abuja Southern Parkway.
A ranar May 28, 2024 ne bayan kammala titin Abuja Southern Parkway...
Wani likitan Najeriya da ya koma da zama a kasar Ingila me suna, Dr. Kelvin Alaneme ya bayar da labarin yanda ya karkare da turin bari a kasar Ingila.
Yace a shekarar 2019, ya jw kasar Ingila duk da shi likita ne a Najeriya amma bai samu lasisin yin aikin likitanci a kasar Ingilar ba.
Yace haka suka hadu shi da wani abokinsa me suna Surya suka rika neman yanda zasu yi tare.
Yace kudinsa na karewa kuma gashi yana bukatar ya mayar da iyalansa zuwa Ingila, yasan cewa idan bai samu aikin yi ba akwai matsala.
Yace a haka wata rana ya kira Surya yace tunda dai aikin ofis ya ki samuwa su je su nemi koma wane irin aiki ne su yi.
Yace haka suka rika bi shago-shago suna tabayar ko zasu samu aiki amma ana ce musu babu.
Yace sun kusa kammala titin gaba daya sai suka shiga shagon wani...
An bayyana yankunan da suka fi yawan yaran da basa zuwa makaranta a Najeriya.
Kafar Statisense da UNICEF ne suka bayyana wadannan bayanai kamar haka:
North West — 8.04 millionNorth East — 5.06 millionNorth Central — 2.12 millionSouth West — 1.15 millionSouth South — 769KSouth East — 664K
Northern Nigeria — 15.23 millionSouthern Nigeria — 2.58 million
Wani bincike ya bayyana yankunan da suka fi yin Jima'i ba tare da Kwaroron ribaba.
Yankuman sune kamar haka:
North East — 70.6%South South — 67.0%North West — 64.4%South West — 63.1%South East — 61.6%North Central — 59.9%
Sai kuma yankunan da suka fi yin jima'i da mutane daban-daban. Suma sune kamar haka:
North East — 72.8%South South — 68.7%South West — 68.2%North Central — 62.9%South East — 65.6%North West — ****
Kafar Statisense ce ta gudanar da wannan bincike.
An bayyana garuruwa 18 a Najeriya da suka fi sauran karfin tattalin arziki.
Lafar StatiSense ce ta bayyana hakan:
Ga garuruwan kamar haka:
Legas
Abuja
Jos
Aba
Enugu
Maiduguri
Owerri
Onitsha
Kano
Ilorin
Kaduna
Sokoto
Zaria
Ibadan
Fatakwal
Abeokuta
Ogbomosho
Benin City.