Wednesday, May 13
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Dolene Godswill Akpabio ya sauka ko mu tsigeshi>>Inji Sanata Adams Oshiomhole

Dolene Godswill Akpabio ya sauka ko mu tsigeshi>>Inji Sanata Adams Oshiomhole

Duk Labarai
Sanata Adams Oshiomhole ya caccaki kakakin majalisar Dattijai Godswill Akpabio saboda canja dokokin zama kakakin majalisar. Adams Oshiomhole yace sabuwar dokar dake cewa sai mutum yayi shekaru 8 a matsayin sanata a jere kamin ya nemi shugabancin majalisar bata yi ba. Yace idan kuwa aka ce za'a yi amfani da wannan doka to shi kamshi Sanata Godswill Akpabio dole ya sauka daga mukaminsa dan bai cika sharudan ba. Yace kakakin majalisa da suka gabata irin su David Mark da sauransu sun yi shugabancin majalisar da dokokin da ake dasu ba tare da matsala ba. Yace to a wane dalili za'a canja dokokin? https://twitter.com/i/status/2052466231807185068
Kalli Bidiyon: Yanda magidanci ya kama wani babban mutum da matarsa

Kalli Bidiyon: Yanda magidanci ya kama wani babban mutum da matarsa

Duk Labarai
Wannan wani magidanci ne ya kama wani babban mutu da matarsa a cikin mota a Otal An jishi yana cewa na gargadeka ka daina bin matata amma ka kiya. A Bidiyon da ya watsu a kafafen sada zumunta, an ga mutane da yawa na goyon bayan mijin. Cin Amanar Aure wani lamari ne dake ciwa wasu ma'auratan tuwo a kwarya wanda idan asiri ya tonu irin wana sai kaga an ji Kunya. https://twitter.com/i/status/2052431698021793849
Da Duminsa: Tsohon Ministan wutar Lantarki, Saleh Mamman ya tsere bayan da kotu ta daureshi bisa satar Naira Biliyan 33

Da Duminsa: Tsohon Ministan wutar Lantarki, Saleh Mamman ya tsere bayan da kotu ta daureshi bisa satar Naira Biliyan 33

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon Ministan Wutar Lantarkin, Saleh Mamman ya tsere bayan da kotu ta daureshi bisa satar Naira Biliyan 33.8. Daya daga cikin lauyoyin da suka halarci zaman kotun na yau ne ya bayyana cewa, Saleh Mamman yaki bayyana a gaban kotun da gangan. Yace kuma tuni kotu tasa a nemo mata shi ruwa a jallo. https://twitter.com/i/status/2052402759450660998
Da Duminsa:Wata kungiyar matasa magoya bayan Peter Obi sun ce a yanzu basa son Peter Obi, Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan suke son ya tsaya takara

Da Duminsa:Wata kungiyar matasa magoya bayan Peter Obi sun ce a yanzu basa son Peter Obi, Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan suke son ya tsaya takara

Duk Labarai
Wata Kungiyar matasa magoya bayan Peter Obi sun bayyana cewa, a yanzu basa son Peter Obi, tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan suke son ya fito ya sake tsayawa takarar shugaban kasa a 2027. Matasan sun ce ya zamarwa Goodluck Jonathan dole ya amince da wannan bukata tasu. A dasu ne dai wasu matasa suka je kofar gidan tsohon shugaban kasar inda suke kiran da ya fito takarar shugaban kasa amma yace zai yi shawara tukuna. https://twitter.com/i/status/2052376514843275418
Kai Duniya: Ashe Bidiyo kala 4 ne suka fita na Halima da Saurayinta ya fitar

Kai Duniya: Ashe Bidiyo kala 4 ne suka fita na Halima da Saurayinta ya fitar

Duk Labarai
Rahotanni sun tabbatar da cewa, Bidiyon daidai har guda 4 ne na aikata Alfasha na wata matashiya Halima ya fito. Da farko dai da yawa sun dauka Bidiyo daya ne inda ake ta tausaya mata musamman yanda ake jin tana kiran babanta da mamanta. Saidai daga baya an gano Bidiyo hudu ne. Wakilin Hutudole yayi kachibus da Bidiyon amma ba zamu iya wallafa muku suba saboda lamarin yayi matukar muni sosai. Da fatan Allah ya shiryemu baki daya.
Kalli Bidiyon: An daurawa Matasa dake Bidiyon a Tiktok aure

Kalli Bidiyon: An daurawa Matasa dake Bidiyon a Tiktok aure

Duk Labarai
Wannan wasu matasa ne dake Bidiyon dake jawo cece-kuce a Tiktok da aka daurawa Aure. Saidai auren nasu kamar su a wajansu ba da gaske suke ba, shima sun dauka Content ne. Amma duk wani abu da ake yi a aure da ya hada da sadaki, shaidu, da Siga duka an yi. Wannan yawa hakan ya dauki hankula inda ake ta cewa aure ya dauru. https://www.tiktok.com/@muhammadsunnahaljosawy/video/7637104691192663304?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7637104691192663304&source=h5_m&timestamp=1778158548&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&item_author_type=2&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign=client_sha...
Kalli Bidiyon: Daya daga cikin mata masuwa Rarara Amshi na rokon dan Allah a samu wani ya saka mata Sola ko ta dubu dari ce

Kalli Bidiyon: Daya daga cikin mata masuwa Rarara Amshi na rokon dan Allah a samu wani ya saka mata Sola ko ta dubu dari ce

Duk Labarai
Daya daga cikin masu yiwa Rarara Amshi wadda akewa lakabi da Dumdum ta yi rokon cewa, dan Allah a samu wani ya saka mata Solar ko da ta dubu 100 ce. Ta fito ta bayyana hakane q shafinta na Tiktok inda ta nuna fankarta data kai gyara. https://www.tiktok.com/@dumdum8109/video/7636503551467949333?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7636503551467949333&source=h5_m&timestamp=1778157585&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&item_author_type=2&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign=client_share&utm_medium=android&share_iid=7625183675001341712&share_link_id=4d4d6053-36e7-41aa-b9d1-96fd0...
Da Duminsa: Kotu ta daure tsohon Ministan wutar Lantarki Sale Mamman saboda satar Naira Biliyan 33.8

Da Duminsa: Kotu ta daure tsohon Ministan wutar Lantarki Sale Mamman saboda satar Naira Biliyan 33.8

Duk Labarai
Babbar kotun tarayya dake Abuja ta daure tsohon Ministan wutar Lantarkin, Saleh Mamman bisa satar Naira Biliyan 33.8 A yau Alhamis ne kotun ta daureshi inda ta sameshi da aikata laifuka 12 wanda kotun tace bisa hujjojin da aka gabatar mata, ta gamsu cewa ya aikata laifukan. Mai Shari'a, James Omotosho ne ya yanke wannan hukunci duk da cewa Saleh Mamman bai samu damar halartar wajan shari'ar ba.