Monday, February 23
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Da Duminsa: A karshe dai majalisar Wakilai ta amince da dakatarwar da Shugaba Tinubu yawa Gwamnan jihar Rivers

Da Duminsa: A karshe dai majalisar Wakilai ta amince da dakatarwar da Shugaba Tinubu yawa Gwamnan jihar Rivers

Duk Labarai
Rahotanni daga majalisar tarayya na cewa, majalisar Dattijai ta amince da dakatarwar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yawa gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara. Majalisar data samu zaman 'yan majalisar su 243 ta yiwa dokar garambawul. Ta bayar da shawarar a kafa kwamiti wanda zai tabbatar da samun zaman lafiya a jihar ta Rivers. Sannan kuma a baiwa majalisar ta tarayya karbar aikin gudanar da majalisar jihar Rivers na tsawon watanni 6 da aka dakatar da ita.
Da Duminsa:Atiku, El-Rufai, Peter Obi, Rotimi Amaechi sun hada kai dan yakar Tinubu a zaben 2027

Da Duminsa:Atiku, El-Rufai, Peter Obi, Rotimi Amaechi sun hada kai dan yakar Tinubu a zaben 2027

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Rahotannin da muke samu na cewa, tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar da tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai da sauran manyan mutane na APC sun hada kai dan ganin sun kayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben shekarar 2027 me zuwa. A cikin hadakar akwai kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 karkashin jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, wanda Yunusa Tanko ya wakilta, akwai kuma tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal. Wadand...
Wasu na ta tambayar wai Ina Kwankwasone, kowane babban dan Adawa yayi Allah wadai da dakatar a Gwamnan Rivers amma har yanzu shi bai ce komai akai ba

Wasu na ta tambayar wai Ina Kwankwasone, kowane babban dan Adawa yayi Allah wadai da dakatar a Gwamnan Rivers amma har yanzu shi bai ce komai akai ba

Duk Labarai
A yayin da siyasar Najeriya ta mayar da hankali kan dakatar da gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara, manyan 'yan Adawa na ta Allah wadai da wannan mataki na shugaban kasa. Atiku Abubakar, Peter Obi, Nasiru El-Rufai, da sauran manyan 'yan Adawa duk sun fito suna ta Allah wadai da wannan mataki, saidai ba'a ji duriyar Tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ba. Daya daga cikin wadanda suka bayyana irin wannan ra'ayi shine Comrade Adnan. Ya bayyana cewa, duk da shirun Kwankwaso akan lamari irin wannan amma haka mutane ke kiransa da Jagora. Abin dai jira a gani shine ko Kwankwaso zai yi magana akan lamarin.
Karuwanci ya kaita jihar Legas>>Hadimin Shugaban kasa ya zargi matashiya ‘yar Bautar kasa data soki Shugaba Tinubu

Karuwanci ya kaita jihar Legas>>Hadimin Shugaban kasa ya zargi matashiya ‘yar Bautar kasa data soki Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Hadimin shugaban kasa, Tope Fasua ya zargi matashiya me bautar kasa,  ‘Raye’ Uguamaye da cewa Karuwancine ya kaita jihar Legas. Wannan zargi nashi na zuwane bayan da sunan matashiyar ya yadu sosai a kafafen sadarwa bayan da ta soki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. A sakon da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Tope yace matashiyar ta je legas ne dan samun rabonta na Naira Biliyan N661. Kwanannan ne aka bayyana cewa mazan Legas sun kashe Naira Biliyan N661 wajan biyan bukatarsu da karuwai. A baya dai, wani hadimin shugaban kasar me suna Temitope Ajayi ya nemi a kaddamarwa matashiya Raye da hukuncin kisa saboda sukar shugaban kasar. Saidai daga baya ya fito ya bayyana cewa, shi ba haka yake nufi ba.
Dakatarwar da nawa Fubara taimakonsa na yi, dan da ban dakatar dashi ba da Tuni majalisar jihar Rivers ta tsigeshi>>Shugaba Tinubu

Dakatarwar da nawa Fubara taimakonsa na yi, dan da ban dakatar dashi ba da Tuni majalisar jihar Rivers ta tsigeshi>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, dakatarwar da yawa Gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara ce ta hana majalisar jihar tsigeshi a matsayin gwamna. Ya bayyana haka ta bakin lauyan Gwamnati, kuma Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi inda yace da basu dakatar da Gwamna Fubara ba da tuni an tsigeshi. Yace kuma da an tsigeshi da shikenan yayi batan bakatantan. Yace amma dakatarwar ta Fubara wata dabara ce ta hana tsigeshi. Shugaba Tinubu dai ya dakatar da Gwamna Fubara har na tsawon watanni 6.
A cikin Azumin Watan Ramadana, An kama dan shekaru 35, Abdullaziz Mohammed da yiwa karamar yarinya me shekaru 5 fyade a jihar Adamawa

A cikin Azumin Watan Ramadana, An kama dan shekaru 35, Abdullaziz Mohammed da yiwa karamar yarinya me shekaru 5 fyade a jihar Adamawa

Duk Labarai
'Yansanda a jihar Adamawa sun kama dan shekaru 35 Abdullaziz Mohammed da zargin yiwa karamar yarinya me shekaru 5 fyade a jihar. Kakakin 'yansandan jihar, CSP Suleiman Nguroje ne ya bayyana haka inda yace lamarin ya farune a karamar hukumar Mubi dake jihar. Yace mahaifin yarinyar me ya kai musu kara ranar March 17, 2025 inda yace Abdulaziz ya ja diyarsa zuwa cikin wani dakin da ake Nika a Kasuwar Barkono dake Mubi ya mata fyade. Tuni dai aka tafi da yarinyar zuwa Asibiti. Yayin da shi kuma wanda ake zargi ya amsa laifinsa. Kwamishinan 'yansandan jihar yayi Allah wadai da lamarin inda ya aika da wanda ake zargi zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar.
Dakatarwar da Shugaba Tinubu yawa Gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara na Tangal-Tangal yana ta neman ‘yan Majalisa su amince masa domin idan basu amince ba dole ya janye dakatarwar

Dakatarwar da Shugaba Tinubu yawa Gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara na Tangal-Tangal yana ta neman ‘yan Majalisa su amince masa domin idan basu amince ba dole ya janye dakatarwar

Duk Labarai
Rahotanni sun bayana cewa, dakatarwar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya wa gwamnan jihar Rivers Simi Fubara na Tangal-Tangal. Dalili kuwa sai an samu biyu bisa uku na 'yan majalisar dattijai dana majalisar wakilai duka sun amince masa kamin wannan dakatarwa ta tabbata. A yanzu haka rahotanni, kamar yanda jaridar TheCable ta ruwaito na cewa, wakilan shugaban kasar sai kai kawo suke a tsakanin 'yan majalisar dan ganin sun samo kansu sun amince da dakatar da Gwamnan jihar Rivers din. Saidai matsalar itace mafi yawanci 'yan majalisar basa Najeriya, da yawansu sun je aikin Umrah inda wasu ke wasu kasashen. Hakanan wata matsala itace banda 'yan majalisar dake jam'iyyun Adawa, har wadanda ke jam'iyyar APC an samu suna nuna rashin amincewa da wannan dakatarwar da akawa Gwamnan ji...
Bamu san da zaben kiranye da akewa Sanata Natasha Akpoti ba>>Inji INEC

Bamu san da zaben kiranye da akewa Sanata Natasha Akpoti ba>>Inji INEC

Duk Labarai
Hukumar zabe me zaman kanta, INEC wadda itace ke da alhakin gudanar da zaben yin kiranye na duk wani zababben dan siyasa tace bata san da maganar zaben kiranye da akewa Sanata Natasha Akpoti ba. A jiyane dai Bidiyo da hotuna suka bayyana inda aka ga mutane da yawa a mazabar sanata Natasha Akpoti suna gudanar da abinda aka kira da zaben kiranye dan ta dawo gida ta daina wakiltarsu a majalisar Dattijai. An gudanar da zaben yanke kauna ga Sanata Natasha Akpoti a karamar hukumar Okehi dake jihar. Wani me suna Nura Abdullahi da aka yi hira dashi game da lamarin yace suna zabenne dan Sanata Natasha Akpoti bata wakiltarsu da kyau sannan kuma ta kasa magance matsalolin talauci, Ilimi da gyaran abubuwan more rayuwa. Saidai an gano cewa an yaudari mutanene da cewa za'a basu tallafine amm...
An kai karin jami’an tsaro dubu 10 Jihar Rivers bayan dakatar da Gwamna Fubara

An kai karin jami’an tsaro dubu 10 Jihar Rivers bayan dakatar da Gwamna Fubara

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Rivers na cewa,karin jami'an tsaron Civil Defense dubu 10 ne aka kai jihar Rivers dan su samar da tsaro bayan dakatar da Gwamna Fubara. Rahotannin sun ce an kai jami'an tsaronne dan su hadu da sojoji da sauran jami'an tsaron dake jihar dan su samar da tsaro ga bututun man fetur dake jihar. Kakakin hukumar ta Civil Defense, Afolabi Babawale ya tannatar da hakan, yayi kira da a daina fasa bututun man inda yace jami'ansu dubu 10 ne aka kai jihar ta Rivers dan su hana hakan. Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dai ya dakatar da Gwamna Fubara bayan da aka fasa bututun man fetur a jihar har sau 3.