Friday, March 20
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Bidiyo:Yanda aka kama Wani Fasto wanda da ya gama wa’azi da rana a coci, sai ya koma da dare ya zama boka yana sihiri da sassan jikin mutane

Kalli Bidiyo:Yanda aka kama Wani Fasto wanda da ya gama wa’azi da rana a coci, sai ya koma da dare ya zama boka yana sihiri da sassan jikin mutane

Duk Labarai
Asirin Wani Fasto wanda asalinsa Boka ne dake sihiri da sassan jikin mutane ya tonu. Sunan Faston Onye Eze Jesus inda wasu jami'an tsaro da suka so kamashi suka je masa a matsayin wadanda ke son su yi kudi. Ya mince zai yi musu tsafi da sassan jikin mutum dan biyan bukatarsu. https://www.youtube.com/watch?v=jQWWp-mHe8w&pp=ygUVT255ZSBFemUgSmVzdXMgYXJyZXN0 An kamashine a jihar Anambra inda kuma ya amsa laifinsa.
Bayan da ya koma APC, shugaba Tinubu ya baiwa Sanata Shehu Sani mukamin Jakada

Bayan da ya koma APC, shugaba Tinubu ya baiwa Sanata Shehu Sani mukamin Jakada

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya fitar da sunayen mutanen da zai baiwa aikin jakadancin Najeriya zuwa kasashen waje. Tuni dai aka nemi wadanda sunayensu ya fita cewa su je ofishin DSS na kusa dasu dan a musu bincike kan tsaro sannan su bayar da bayanai kan ayyukan da suka taba yi a baya. Wata majiya me karfi ta bayyanawa jaridar Vanguard cewa akwai sunan Shehu Sani wanda bai dade da komawa jam'iyyar APC ba cikin wadanda aka baiwa mukamin sanatan. Sannan akwai tsaffin gwamnonin jihohin inyamurai watau Ifeanyi Ugwuanyi da Okezie Ikpeazu. Sannan majiyar tace akwai sunan Femi Fani Kayode sannan kuma akwai sunan Reno Omokri.
NDLEA Ta Cafke Shàķikai Biyu Dà Hodar Ìbĺìś Kilo 5 A Filin Jiŕgin Sàma Na Lagos Yayin Shirin Su Na Tafiya Zuwa Indiya

NDLEA Ta Cafke Shàķikai Biyu Dà Hodar Ìbĺìś Kilo 5 A Filin Jiŕgin Sàma Na Lagos Yayin Shirin Su Na Tafiya Zuwa Indiya

Duk Labarai
NDLEA Ta Cafke Shàķikai Biyu Dà Hodar Ìbĺìś Kilo 5 A Filin Jiŕgin Sàma Na Lagos Yayin Shirin Su Na Tafiya Zuwa Indiya Yayin da aka kama matashi ɗan birtaniya da kwayar loud filin jirgi; tsoho mai shekaru 75 da Skunk a Abia; tare da lalata fiye da kilo dubu 250 na tabar wiwi a Cross River Dakarun runduna ta musamman na Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa, wato NDLEA, sun kama wasu ‘yan uwan juna guda biyu: John Abugu mai shekaru 43 da Kenneth Abugu mai shekaru 31 a filin jirgin sama na Murtala Muhammed International Airport (MMIA) da ke Ikeja, Legas. An kama su da hodar Iblis mai nauyin kilo 5 da aka ɓoye a bangon jakunkuninsu, yayin da suke ƙoƙarin shiga jirgin sama zuwa kasar Indiya. An cafke su ne a ranar Alhamis 3 ga Afrilu, 2025, bayan samun sahihan bayanan si...
Majalisar Kula Da sarautun Gargajiya A Nijeriya Ta Nuna Damuwa Kan Gayyatar Da Aka Yi Wa Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II

Majalisar Kula Da sarautun Gargajiya A Nijeriya Ta Nuna Damuwa Kan Gayyatar Da Aka Yi Wa Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II

Duk Labarai
Majalisar Kula Da Cibiyoyin Gargajiya A Nijeriya Ta Nuna Damuwa Kan Gayyatar Da Aka Yi Wa Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II Ƙungiyar ta yi nuni da cewa tuni rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta fara gudanar da bincike kan lamarin, wanda hakan ya sa gayyatar ‘yan sandan bai zama dole ba. Ƙungiyar a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun ko-odinetan ta na ƙasa Alhaji Yahaya Nda Musa, ta bayyana mamakin gayyatar da ‘yan sandan suka yi mai dauke da kwanan watan Afrilu 4, 2025, mai ɗauke da sa hannun kwamishinan ‘yan sanda Olajide Rufus Ibitoye, a madadin mataimakin babban sufeton ‘yan sanda mai kula da sashen leken asiri na rundunar. “Muna da ra’ayin cewa wannan gayyata da babbar hukumar ‘yan sanda ta yi wa Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu cin mutunci ne ga cibiyarmu ta gargajiya, ...
Ana zargin Jami’an tsaro na shirin farmakar muhallan Mabiya Shi’a

Ana zargin Jami’an tsaro na shirin farmakar muhallan Mabiya Shi’a

Duk Labarai
A wani rahoto da jaridar Sahara Reporters ta ruwaito ya nuna cewar, ana zargin gamayyar jami'an tsaron Nijeriya suna shirin kai mummunan hari wasu gurare guda biyar cikin muhallan yan Harkar Musulunci kamar yanda majiyar ta bayyana. Majiyar ta kuma shaida ma jaridar Sahara Reporters yadda Gamayyar jami'an tsaron suke ta tattaunawa da sauran jami'an a karkashin kasa, suna faɗa musu su kwana cikin shiri domin gudanar da aikin da zasu yi a cikin daren Litinin da misalin karfe 2 na daren nan. A makon data gabata ne dai aka yi jana'izar wasu cikin mutanen da sojoji suka kashe masu gudanar da jerin gwano kan lamarin Palasɗinu. Sama da mutane dari uku ne ake tsare dasu a gidajen yarin Kuje dake Abuja da kuma Suleja, wasu kuma suna hannun yan sanda kamar yanda Lauyoyin Harkar Musuluncin s...
Labari Mai Daɗin Ji; Shugaba Tinubu ya amince da samar da sabbin ƙananan asibitoci dubu 8,800 ko’ina a faɗin Nijeriya

Labari Mai Daɗin Ji; Shugaba Tinubu ya amince da samar da sabbin ƙananan asibitoci dubu 8,800 ko’ina a faɗin Nijeriya

Duk Labarai
Shugaba Bola Tinubu ya amince da samar sa sabbin asibitocin sha-ka-tafi guda dubu 8,800 a fadin kasar nan da kuma inganta manyan asibitoci da ake da su don magance cutukan damuwa da cutuka masu yaɗuwa. Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a yau Asabar a lokacin da ya kaddamar da cibiyar kula da cutar damuwa ta Sulaiman Adebola Adegunwa a garin Sagamu na jihar Ogun. Mataimakin shugaban kasar, a wajen taron, ya yi kira da a kara samar da asibitoci masu zaman kan su a wani ɓangare na sauye-sauyen da gwamnatin ke yi a fannin kiwon lafiya da ci gaban kiwon lafiya a fadin Najeriya. Ya jaddada kudirin Gwamnatin Tarayya na magance matsalolin da ake fuskanta a fannin kiwon lafiya ta hanyar dabarun hadin gwiwa da zuba jari, yana mai cewa bude asibitoci masu z...
Kamfanonin sufurin maniyyatan Najeriya sun janye daga aikin hajjin bana

Kamfanonin sufurin maniyyatan Najeriya sun janye daga aikin hajjin bana

Duk Labarai
A Najeriya, wasu kamfanonin sufurin hajji da umarah na Najeriya sun bayyana janyewarsu daga hada-hadar aikin hajjin bana, saboda yadda suka ce hukumar alhazan Najeriyar tana gudanar da wasu ayyuka da kamfanonin ya kamata su riƙa aiwatarwa. Malam Haruna Isma'il shugaban ɗaya daga cikin kamfanonin uku, ya ce sun kwashe tsawon shekara uku suna neman a yi gyara, amma ba a yi komai ba. Malam Haruna Isma'il shugaban kamfanin harkar sufurin hajji da umarah na Annur Air Services ya karan-tsaye da wuce gona da iri da acewarsa suke cutar da alhazai da masu harkar jigilar ne suka sa suka yanke shawarar janyewa daga aikin. Mun dai nemi jin ta bakin jami'ar hulɗa da jama'a ta hukumar alhazai ta Najeriya, wadda ta yi alƙawarin aiko mana da nasu martanin kan wannan batu, amma har ya zuwa yanzu b...
An kashe ƴan China biyu a jihar Abia

An kashe ƴan China biyu a jihar Abia

Duk Labarai
Rundunar ƴansandan jihar Abia da ke kudu maso kudancin Najeriya ta tabbatar da kashe wasu ƴan ƙasar China guda biyu da wani ɗansanda mai ba su kariya. Rundunar ta ce ƴansanda sun ɗauki ne bayan rundunar ta samu kiran kar-ta-kwana cewa wasu gungun mahara sun kai wa ƴan Chinan da ƴansanda da ke rakiya hari a hanyarsu ta zuwa kamfaninsu da ke titin Agukwu-Amaya a garin Ndundu a ƙaramar hukumar Isuikwuato na jihar. A wata sanarwa da tashar Channels ta ruwaito daga kakakin rundunar ƴansandan jihar, Maureen Chinaka yana cewa an kashe Mista Quan wanda shi ne manajan kamfanin da Mista Cai abokin aikinsa da Insfekta Audu Saidu. Rundunar ta ƙara da cewa jami'anta sun samu nasarar ceto wasu ƴan China huɗu da ƴansanda guda biyu. A sanarwar, kwamishinan yansandan jihar, Danladi Is...