Hukumar tace finai finai ta jihar Kano ta dakatar da nuna fim din ‘Labarina’ da gidan Sarauta da wasu karin fina finai 20
Hukumar tace finai finai ta jihar Kano ta dakatar da nuna fim din 'Labarina' da gidan Sarauta da wasu karin fina finai 20
A kokarinta na tabbatar da ana bin dokar tace fina-finai sauda kafa tare da kara dora masana'antar kannywood a kan saiti, Hukumar tace fina-finai da Dab'i ta Jahar Kano karkashin jagorancin Alh Abba El-mustapha ta dauki wani gagarun mataki domin tsaftace yadda ake sakin fina-finai barkatai batare da cika ka'idar da doka ta tanadar musu ba na kawo kowanne film gabanta a tantance shi kafin ya isa ga idanun al'umma inda ta dakatar da wasu Manyan Fina-finai har guda 22 daga sakasu a kafafen Internet ko gidan TV
Abba El-mustapha ne ya bayyana wannan mataki biyo bayan tattaunawa da manyan jami'an Hukumar tare da dogon nazari domin kawo karshen korafe korafen da Hukumar ...








