Ji yanda ta kaya tsakanin Tsohon Minista, Sheikh Isa Ali Pantami da wani daya zargeshi da Shyekye Kirista a ATBU
Wani ya zargi Tsohon Minista, Malamin Addinin Islama, Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami da sawa a Shyekye wani kirista a jami'ar ATBU.
Saidai malam ya mayar masa da martanin cewa wannan zancen karyane dan bai taba kashewa ba kuma bai taba sawa a kashe wani ba.
Mutumin ya kawo Rahoton jaridar Punchng da hotunan dalibin da ake zargin malam akai.
Saidai malam yace idan mutumin yana jin yana da hujja akan wannan zargi nasa, ya kai kotu ko kuma ya bayar da cikakkun bayanansa dan shi malam ya kaishi kotu a yi shari'a, malam yace kaga a haka ma idan zargin da ake masa da gaskene, shi mutumin ya taimaki iyalan mamacin kenan sai a hukuntashi.
Saidai wasu sun rika baiwa malam Shawarar ya maka jaridar ta Punchng a kotu da wanda ya masa wannan zargi.
Amma wasu sun baiwa malam shawarar cew...








