Friday, February 20
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Makaranta a Najeriya ta kori ɗalibar da ta fallawa malami mari kan ya hanata TikTok

Makaranta a Najeriya ta kori ɗalibar da ta fallawa malami mari kan ya hanata TikTok

Duk Labarai
Hukumomin Jami'ar Nnamdi Azikiwe da ke, Awka a jihar Anambra ta kori ɗalibar nan, Goddy-Mbakwe Chimamaka Precious, saboda cakuma tare da cin kwalar wani malamin jami'ar. A cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta an ga ɗalibar ta far wa malamin jami'ar, Dr Chukwudi Okoye, bayan ya ratsa ta cikin bidiyon da take ɗauka a wani lungu da ke harabar jami'ar. Cikin takardar korar da jami'ar ta fitar mai ɗauke da kwanan watan 13 ga watan Fabrairu, wadda magatakardar jami'ar, Victor I. Modebelu ya sanya wa hannu, ta ce an ɗauki matakin ne bayan shawarar kwamitin bincike da jami'ar ta kafa. ''Kwamitin ya samu ɗalibar da laifin saɓa wa dokokin ladabtarwa na jami'ar, musamman sashe na 4 na dokar ladabtarwa ta (SDR)'', in ji takardar korar, kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito. ...
An ɗage taron mahaddata Qur’ani da aka shirya yi a Abuja

An ɗage taron mahaddata Qur’ani da aka shirya yi a Abuja

Duk Labarai
Bayanan da BBC ta samu sun nuna cewa an ɗage taron mahaddata al-Qur'ani da ake yi wa laƙabi da Qur'anic Convention a Turance da ya rage ƙasa da mako biyu a gudanar a Abuja, babban birnin Najeriya. An dai saka ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu na 2025 da ranar da za a yi taron da ake sa ran zai samu mahalarta waɗanda mahaddata Qur'ani ne sama da dubu 60 daga ciki da wajen Najeriya. Wani ɗan kwamitin tsara taron wanda bai so a ambaci sunansa ba ya shaida wa BBC cewa "tun daren jiya Alhamis aka ɗage yin wannan taro. Sai dai kuma majiyar ba ta tabbatar wa da BBC haƙiƙanin dalilin da ya sa aka ɗage taro ba da kuma yaushe ne sabon lokacin da za a yi taron a nan gaba. "Ana sa ran sai bayan Ramadan." In ji majiyar. Manufar taron Taron dai wanda tuni allunan tallansa suka cika man...
Makaman da muke dasu zasu iya lalata duniya sau 100>>Inji Shugaban Amurka, Donald Trump

Makaman da muke dasu zasu iya lalata duniya sau 100>>Inji Shugaban Amurka, Donald Trump

Duk Labarai
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya nemi yin taro da kasashen Duniya wanda suka hada da China, da Rasha inda yace zai bayar da shawarar su taru su 3 din suk su rage yawan makaman da suke dasu. Shugaban yace maimakon kashe makudan kudaden da suke akan tsaro, kamata yayi su mayar da hankali wajan kashe irin wadanna kudaden akan ayyukan ci gaban wa mutanen kasarsu. Yace zai nemi duka su ukun su rage kashe kudi akan tsaro da kaso 50 cikin 100 watau su raba kudin gida biyu inda yace yayi amannar kuma zasu amince. Trump yace a yanzu Amurka na da makamai na kare dangi wanda zasu iya lalata Duniya har sau 100 dan haka babu bukatar a ci gaba da kera makaman kare dangi. Ya bayyana hakane a ganawar da yayi da shugaban India, Nedradi Modi.
Dana ya zautu, ku roki Natasha ta kyaleshi, Mahaifiyar 2face ta magantu

Dana ya zautu, ku roki Natasha ta kyaleshi, Mahaifiyar 2face ta magantu

Duk Labarai
Mahaifiyar shahararren mawakin Najeriya, 2face Idibia, Rose Idibia ta roki cewa a yi magana da sabuwar Budurwar dan nata 'yar majalisar jihar Edo, Natasha ta kyale danta. Rose ta bayyana hakane a wani faifan bidiyon da ta saki. Tace dan nata yana kokarin sakin matarsa, Annie amma dai tasan cewa, baya cikin hayyacinsa, tacewa Natasha ta cire sakar data ratayawa dan nata dan ya dawo hayyacinsa. 2face Idibia dai ya rabu da matarsa, Annie inda ya koma soyayya da sabuwar budurwarsa,Natasha kuma yace ita zai aura.
Mawakin Najeriya, 2face Idibia ya saki matarsa da suka dade tare ya koma soyayya da ‘yar majalisar jihar Edo, Natasha

Mawakin Najeriya, 2face Idibia ya saki matarsa da suka dade tare ya koma soyayya da ‘yar majalisar jihar Edo, Natasha

Duk Labarai
Tauraron mawakin Najeriya, 2face Idibia ya rabu da matarsa, Annie wadda suka dade tare hadda yara inda a yanzu ya fara soyayya da 'yar majalisar jihar Edo, Natasha Osawaru. 2face ya fito ya bayyanawa Duniya cewa yanzu wadda yake so kuma yake da burin aure itace Natasha Osawaru kuma kada mutane su zargeta da cewa itace silar rabuwarsa da matarsa. https://www.tiktok.com/@beautyqueen_5l/video/7470714448022441238?_t=ZM-8tsO4RaZaFC&_r=1 Bisa Al'adar mutanen kudu, 2face ya nemi Natasha ta aureshi kuma tuni ta amince masa da hakan. Tuni 2face ya baiwa Natasha Zoben Alkawari Lamarin da ya jawo cece-kuce sosaia kafafen sada zumunta.
Wallahi sai da ka dirkawa matarka cikin shege kamin ka aureta kuma idan kace karya nake ka kaini kotu ina da hujja>>Wata Budurwa ta gayawa dan Tsohon Gwamnan Kaduna, Bashir El-Rufai

Wallahi sai da ka dirkawa matarka cikin shege kamin ka aureta kuma idan kace karya nake ka kaini kotu ina da hujja>>Wata Budurwa ta gayawa dan Tsohon Gwamnan Kaduna, Bashir El-Rufai

Duk Labarai
Takaddama ta barke tsakanin wata budurwa da dan gidan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Bashir El-Rufai a dandalin X wanda a baya ake kira da Twitter. Budurwar dai me amfani da sunan Felexible Queen ta mayarwa da Bashir Martanine akan maganar da yayi ta shagube kan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu inda tace tasan Shugaba Tinubu ya baiwa 'ya'yansa tarbiyya ba zasu fito suna cin zarafin mutane ba. Ta jawo hankalin Tsohon gwamnan da cewa ya yiwa dan nasa magana kan abinda yake aikatawa. Saidai lamarin ya kazance bayan da bashir ya mayar mata da martanin cewa, tana yawo otal-otal tana biyawa tsaffin mutane da suka kai sa'annin babanta bukata. Ta mayar mai da martanin cewa shi Jahili ne marar addini i da tace kawai zai yi mata kazafine amma bashi da hujja inda ta kara da cewa, "You ...
Kalli Yanda daliba ta mari malaminta saboda ya mata magana akan Bidiyon Tiktok

Kalli Yanda daliba ta mari malaminta saboda ya mata magana akan Bidiyon Tiktok

Duk Labarai
Wata daliba a jami'ar Nnamdi Azikiwe University dake Awka jihar Anambra ta mari malaminta sannan ta cijeshi. Dalibar dai tana daukar bidiyon Tiktok ne sai malamin ya zo wucewa ya mata magana tare da dan tureta. Saidai ta juya ta rika zaginsa da gaya masa kalamai marasa dadi inda shi kuma ya nemi ta goge bidiyon da ta dauka. Saidai ta ki inda ta cukumeshi ta mareshi ta kuma cijeshi, a karshe dai da kyar aka kwaceshi a hannunta inda sai da aka kaishi asibiti. Tuni dai makarantar ta sanar da cewa ta dauki matakin yin bincike akan lamarin kamin tasan hukuncin da zata yanke. Kalli Bidiyon faruwar lamarin anan
Na yi nadamar yiwa Tinubu yakin neman zabe, Jama’a ku yafe min kan jawo hankalinku da na yi kuka zabeshi>>Dan Balki Kwamanda

Na yi nadamar yiwa Tinubu yakin neman zabe, Jama’a ku yafe min kan jawo hankalinku da na yi kuka zabeshi>>Dan Balki Kwamanda

Duk Labarai
Dan siyasa a jiar Kano, Dan Balki Kwamanda ya bayyana nadama kan jawo hankalin mutane da yayi suka zabi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a matsayin shugaban kasa. Yace yayi nadamar yakin neman zaben da yawa Tinubu. Yace tunda yake a rayuwarsa bai taba yin abinda yayi nadamarsa sosai ba kamar yiwa Tinubu yakin neman zabe. Yace dalili kuwa shine alkawuran da Bola Ahmad Tinubu ya dauka be cika ba kuma mutane na cikin matsananciyar wahala. Ya bayyana hakane a watan hira da gidan Jaridar Daily Trust suka yi dashi inda yace yana neman yafiyar wadanda ya yaudara.