Tuesday, March 17
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Karamin yaro dan shekaru 4 ya kkàshè kansa ta hanyar hàrbìn kansa da Bìndìgàr iyayensa da yake wasa da ita a cikin mota

Karamin yaro dan shekaru 4 ya kkàshè kansa ta hanyar hàrbìn kansa da Bìndìgàr iyayensa da yake wasa da ita a cikin mota

Duk Labarai
Karamin yaro me shekaru 4 ya harbi kansa da Bindigar iyayensa da ya dauka a mota. Rahoton yace yaron ya harbi kansa a kai ne. Lamarin ya farune a Davenport dake jihar Floridan kasar Amurka. Iyayen yaron Robert Morris da matarsa, Quinta Morris suna shiri ne dan kai 'ya'yansu zuwa cin Pizza inda shi yaron doki ya kaishi ga har ya rika kowa shiga mota ya zauna yana jiran iyayensa su je. Matar tana kan Kwamfuta a yayin da Mijin yake bandaki yana wanka a yayin da lamarin ya faru, matar tace ta ji karar abu inda ta yi tsammanin yaranta ne ke kwaramniya. Ta leka dan ta musu magana amma sai ta tarar da danta me shekaru 11 da me shekaru 7 ne kawai suke wasa. Tan sai ta hango kofar shiga garejin motarsu a bude aikuwa tana lekawa sai ta ga dan nata a kwance, da harbin bindiga akai....

Dalilin da yasa Tinubu yaki baka Minista shine ka taba zagin Annabi Isa(AS), sannan An zarge ka da hannu a kkàshe ‘yan Shi’a, sannan kuma ka yi barazanar kkàshè Turawa>>Reno Omokri ya mayarwa da El-Rufai Martani

Duk Labarai
Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri ya bayyana dalilan da suka sa Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai bai tsallake tantancewar zama minista da majalisa ta masa ba. Wannan martani na zuwa bayan da El-Rufai a hirar da yayi da gidan talabijin na Arise TV yace ba majalisa ce taki tantanceshi ba, Tinubu ne ya canja ra'ayi game da mukamin da yaso ya bashi. Reno Omokri wanda a yanzu ya shiga sahun masu kare gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa majalisar tarayya ta gudanar da bincike a cikin gida da kasashen waje kan Nasir El-Rufai kuma binciken nasa bai yi kyau ba shiyasa ba'a bashi mukamin ministan ba. Ya jero laifukan El-Rufai da suka hana a bashi mukamin ministan kamar haka: Yace a ranar Alhamis, February 7, 2019 El-Rufai ya yiwa Turawa masu sa ido...
NAFDAC sun kulle shagunan dake sayar da magungunan jabu

NAFDAC sun kulle shagunan dake sayar da magungunan jabu

Duk Labarai
Hukumar kula da ingancin magunguna da abinci ta Najeriya Nafdac ta ce ta rufe sama da shaguna 11,000 tare da kama mutum 40 a yaƙin da take yi da sayar da ƙwayoyin jabu. Da take yi wa 'yanjarida jawabi a ranar Lahadi, shugabar hukumar Farfesa Mojisola Adeyeye ta ce sun tsara samamen ne tun shekara ɗaya da ta wuce. Zuwa yanzu, Nafdac ta kai samame kasuwanni da dama ciki har da Idumota a Legas, da Ariaria a garin Aba, da Bridge Market a Onitsha a ranar 10 ga watan Fabrairu. Ta ce sun hari kasuwanni uku da ke rarraba kashi 80 cikin 100 na magunguna a Najeriya, kuma sun yi nasarar kamawa tare da ƙwace ƙwayoyin jabu da waɗanda ba a yi wa rajista ba. Farfesar ta kuma sun samu sama da mota 20 ta jabun magunguna a Aba, aƙalla 30 a Onitsha, da wasu 27 a kasuwar Idumota. "Abin da muka ...
Babu shugaban kasar da yana cikin hankalinsa zai jawoka jikinsa saboda yanda ka yi Alfahari da aika Tsohon shugaban kasa, ‘Yar’adua Kabari, Shehu Sani ya gayawa El-Rufai

Babu shugaban kasar da yana cikin hankalinsa zai jawoka jikinsa saboda yanda ka yi Alfahari da aika Tsohon shugaban kasa, ‘Yar’adua Kabari, Shehu Sani ya gayawa El-Rufai

Duk Labarai
Tsohon sanatan kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya mayarwa da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai martani kan maganar da yayi cewa Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu baya son yin aiki dashi. A hirar da aka yi dashi a gidan talabijin din Arise TV, El-Rufai ya bayyana cewa ba majalisa bace ta ki amincewa dashi a matsayin minista ba, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne ya fasa bashi mukamin duk da cewa sun yi alkawari akan hakan. Saidai a wani matsayi na martani ga El-Rufai, Sanata Shehu Sani ya rubuta a shafinsa cewa, Babu shugaban kasa yanzu ko nan gaba dake cikin hayyacinsa zai jawo mutumin da yayi alfahari da aika tsohon shugaban kasa, Umar Musa 'Yar'adua zuwa Kabari. Sanata Sani ya kara da cewa, ai mutum zai yi tunani cewa tunda kawa dan uwanka haka, to lallai b...
Gobara ta ƙone shaguna fiye da 100 a kasuwar Zamfara

Gobara ta ƙone shaguna fiye da 100 a kasuwar Zamfara

Duk Labarai
Wata gobara a babbar kasuwar Gusau da ke jihar Zamfara ta laƙume aƙalla shaguna 103 a ɓangaren kayayyakin abinci masu saurin lalacewa da ke kasuwar. Duk da dai ba a gano dalilin faruwar gobarar ba, ɗaya daga cikin masu kashe gobarar ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa gobarar na da alaƙa da wutar lantarki inda ya ce gobarar ta kama ne jim kaɗan bayan kawo wuta a kasuwar. A cewarsu, gobarar ta soma ne da karfe 10:30 na daren Lahadi kuma ta shafe sa'oi ta na ci kafin ma'aikatan hukumar kashe gobar na jihar da na tarayya suka yi nasarar kashe ta da karfe biyun dare. Shugaban kungiyar masu sayar da kayan abinci da ke saurin lalacewa, Alhaji Inusa Saminu ya shaida wa jaridar ta Daily Trust cewa lamarin ya munana, kuma zuwa yanzu ba za su iya kirga asarar su ba sai dai ya ce sun kai m...
China za ta haramta tsawwala sadakin aure da bikin ‘almubazzaranci’

China za ta haramta tsawwala sadakin aure da bikin ‘almubazzaranci’

Duk Labarai
Gwamnatin ƙasar China ta ci alwashin kawar da al'adar tsawwala sadaki da kuma bikin wadaka da kuɗi. Alwashin, wanda ya fito ta bakin jami'in gwamnati mai kula da lamurran yankunan karkara (Zhu Weidong), na zuwa ne bayan yawan aure da ake ɗaurawa a ƙasar ya ragu sosai a bara. Hukumomi na ganin cewa sadaki mai yawa na dubban daloli da ake yankawa da kuma kayan aure masu yawa da ake buƙata daga wurin maza, na daga cikin abubuwan da ke hana maza yin aure. Sai dai har yanzu hukumomin ba su ɗauki wani mataki kan dokar raba kaya bayan rabuwar aure, wadda ake ganin ta fifita maza.
Ɓangaren Kwankwaso ba shi da hurumin korar mu daga NNPP saboda su ba halastattun shuwagabannin Jam’iyya bane- Kawu Sumaila

Ɓangaren Kwankwaso ba shi da hurumin korar mu daga NNPP saboda su ba halastattun shuwagabannin Jam’iyya bane- Kawu Sumaila

Duk Labarai
Ƴan majalisar dokokin Najeriya da jam'iyyar NNPP reshen jihar Kano ta dakatar sun yi watsi da matakin jam'iyyar, tare da bayyana ta a matsayin wadda "ba ta halasta ba". A yau Litinin ne shugaban jam'iyyar NNPP a jihar ta Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa ya sanar da dakatar da ƴan majalisar huɗu daga jam'iyyar bisa zargin su da ayyukan "zagon ƙasa". A a tattaunawarsa da BBC, Sanata Kawu Sumaila ya ce "ita kanta wannan jam'iyyar da waɗanda suka yi sanarwar, kotu tana cajin su da cewa su ba halastattun shugabannin jam'iyya ba ne, don haka ba su da iko ko damar ɗaukar wannan mataki." A game da batun gayyatar da shugaban jam'iyyar ta NNPP ya bayyana a lokacin sanar da dakatar da ƴan majalisar, Sumaila ya ce "gayyata ce kawai ta zumunci... shi ke nan yanzu jam'iyya sai ta hana ka gayyaci...
Uba Sani da Nuhu Ribadu ba abokaina ba ne yanzu – El-Rufa’i

Uba Sani da Nuhu Ribadu ba abokaina ba ne yanzu – El-Rufa’i

Duk Labarai
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya bayyana cewa 'a yanzu Uba Sani ba abokinsa ba ne' bayan abubuwan da ke faruwa baya-bayan nan. El-Rufa'i ya bayyana hakan ne a tattaunawar da ya gudanar da tashar talabijin ta Arise da yammacin yau Litinin. Bayan kammala wa'adinsa na shekara takwas a matsayin gwamnan jihar Kaduna, tsohon gwamnan na fuskantar bincike kan kuɗaɗe da ake zargin sun yi ɓatan-dabo a lokacin mulkinsa. Lamarin ya haifar da muhawara kasancewar thonon gwamnan na Kaduna, Nasir El-Rufa'i da gwamna mai ci Uba Sani sun kasance masu kusanci a tsawon shekara takwas na mulkin tsohon gwamnan. El-Rufa'i ya bayyana cewa aboki shi ne mutumin da zai kawo maka ɗauki ko a lokacin daɗi ko na tsanani. Ya ce "a yanzu Uba Sani da Nuhu Ribadu ba abokaina ba ne. "Na san c...
Majalisa bata ki tantanceni ba, Tinubu ne ya fasa bani mukamin Minista>>El-Rufai

Majalisa bata ki tantanceni ba, Tinubu ne ya fasa bani mukamin Minista>>El-Rufai

Duk Labarai
Tsohon gwamna jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa majalisar tarayya bata ki amincewa dashi ba a matsayin minista. Yace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne ya fasa bashi mukamin na minista. El-Rufai ya bayyana hakanne a yayin ganawar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV. Maganar nada El-Rufai Minista dai itace abinda ta jawo har aka samu tsamin dangantaka tsakanin El-Rufai da gwamnatin Tinubu.
Da Duminsa: NNPP ta Dakatar da Sen. Kawu Sumaila, Ali Madakin Gini, Kabiru Alhassan Rurum da Abdullahi Sani Rogo daga jam’iyyar

Da Duminsa: NNPP ta Dakatar da Sen. Kawu Sumaila, Ali Madakin Gini, Kabiru Alhassan Rurum da Abdullahi Sani Rogo daga jam’iyyar

Duk Labarai
YANZU-YANZU: NNPP A Kano Ta Dakatar Da Kawu Sumaila Da Rurum Da Ali Madaki Jam'iyyar NNPP a jihar Kano ta dauki matakin ladabtarwa kan wasu mambobinta, ciki har da sanata da 'yan majalisar dokoki, bisa zargin aikata ayyukan da suka sabawa manufofin jam'iyyar. Shugaban jam'iyyar na jihar, Alhaji Hashimu Dungurawa, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano ranar Litinin. Ya ce, daga cikin 'yan majalisar da abin ya shafa akwai Sanata Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta Kudu, Alhaji Abdullahi Sani Rogo, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Rogo, Alhassan Rurum mai wakiltar Rano/Kibiya, da kuma Ali Madakin Gini mai wakiltar mazabar Dala a majalisar wakilai. Shugaban jam'iyyar ya bayyana cewa, jam'iyyar ta nuna rashin jin dadinta kan halayen wasu daga cikin 'yan majalisar tara...