Thursday, April 30
Shadow

Author: Bashir Ahmed

‘Yansanda sun kama wanda suka fito zanga-zangar adawa da tsare-tsaren gwamnatin Tinubu a jihar Yobe

‘Yansanda sun kama wanda suka fito zanga-zangar adawa da tsare-tsaren gwamnatin Tinubu a jihar Yobe

Duk Labarai
A jihar Yobe dake Arewacin Najeriya, 'yansanda sun kama shugaban kungiyar da suka fito zanga-zanga inda suke adawa da sabuwar dokar saka ido akan kafafen sada zumunta da ake son zartaswa. Wanda aka kama din shine Abubakar Jawa wanda shine ya jagoranci masu zanga-zangar na jihar Yobe. Bayan shi, akwai kuma mutane 4 da aka kama tare dashi wanda aka bayyana sunayensu kamar haka, Mohammed Kayeri Adam, Suleiman A. Gambo, Maimuna Abba, and Abubakar Jawa.  Da aka Tuntubi kakakin 'yansandan jihar, Dungus Abdulkarim ya musanta kamen inda yace su suna ma neman masu zanga-zangar ne dan basu kariya.
Matasa sun fito zanga-zangar adawa da tsare-tsaren gwamnatin Tinubu duk da gargadin ‘yansanda

Matasa sun fito zanga-zangar adawa da tsare-tsaren gwamnatin Tinubu duk da gargadin ‘yansanda

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Legas sun bayyana cewa, matasa a jihar Legas din sun fito zanga-zangar adawa da wasu tsare-tsaren gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Haka lamarin yake ma a jihar Rivers, matasa sun fito inda suka hau kan tituna suna nuna rashin amincewarsu da tsare-tsaren gwamnatin musamman dakatar da gwamnan jihar Rivers da kuma dokar sanya ido akan kafafen sada zumunta. 'Yansandan dai sun yiwa matasan rakiya tare da basu Kariya musamman a Legas, a baya dai hukumar ta 'yansanda ta hana matasan fitowa zanga-zangar inda suka ce ba'a sakawa zanga-zangar lokacin da ya dace ba. Hakanan a jihar Oyo, da babban birnin tarayya, Abuja ma, masu zanga-zangar sun fito sun nuna damuwarsu.
Làkùràwà sun yi àjàlìn ‘yan sa-kai 13 a Kebbi, Gwamnan jihar ya kai ziyarar jaje

Làkùràwà sun yi àjàlìn ‘yan sa-kai 13 a Kebbi, Gwamnan jihar ya kai ziyarar jaje

Duk Labarai
Lakurawa sun yi ajalin ‘yan sa-kai 13 a Kebbi Lamarin ya faru a karamar hukumar Augie a yankin Morai bayan da ‘yan sa-kan suka yi kokarin hana Lakurawa daukar dabbobin mutanen yankin. Gwamna Nasir Idris na jihar ta Kebbi a ranar Lahadi ta cikin sakon ta‘aziyya a shafin Facebook, gwamnan ya yi allawadai da harin wanda ya ce ya girgiza shi. Da sayin safiyar yau litinin maigirma Gwamna jihar kebbi Comrd Dr Nasir idris kauran malam Abdullahin Gwandu Tare Da maigirma shugaban hukumar bada Agajin gagawa Ta jahar kebbi Barrister Hon Muhammad bello yakubu Rilisco sun sami isah karamar hukumar mulki Ta Augie wurin Gaisuwar Rasuwa mutanen Da lakurawa suka kashe jiya Allah ya jikansu Da Rahama yasa su Aljana fidausi
Atiku da Peter Obi na son komawa jam’iyyar SDP

Atiku da Peter Obi na son komawa jam’iyyar SDP

Duk Labarai
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar SDP, Prince Adewale Adebayo ya bayyana cewa, Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da na Labour Party, Peter Obi na shirin shiga jam'iyyar su. Ya bayyana hakane a wata ganawa da manema labarai. Prince Adewale Adebayo yace ya samu wannan labari ne daga majiyoyi masu tushe a cikin jam'iyyar tasu. Yace suna maraba da wadannan manyan mutane dake son shiga jam'iyyar su.
WATA SABUWA: Idâɲ Kara Fitòwa Ka Çì Mùtùñcìñ Malamai, Saì Muñ Toñà Maka Asìri, Sakon Shêikh Albanin Gombe Ga Dan Beĺlo

WATA SABUWA: Idâɲ Kara Fitòwa Ka Çì Mùtùñcìñ Malamai, Saì Muñ Toñà Maka Asìri, Sakon Shêikh Albanin Gombe Ga Dan Beĺlo

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} WATA SABUWA: Idâɲ Kara Fitòwa Ka Çì Mùtùñcìñ Malamai, Saì Muñ Toñà Maka Asìri, Sakon Shêikh Albanin Gombe Ga Dan Beĺlo Menene ra'ayinku?
Bobrisky ya shigar da ATM gidan yari ta barauniyar hanya ya cire Naira Miliyan 35 inda ya baiwa ma’aikatan gidan yarin cin hanci suka barshi ya yi ta bushasha

Bobrisky ya shigar da ATM gidan yari ta barauniyar hanya ya cire Naira Miliyan 35 inda ya baiwa ma’aikatan gidan yarin cin hanci suka barshi ya yi ta bushasha

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, shahararren dan daudu, Bobrisky ya shigar da ATM guda 8 cikin gidan yari a lokacin da ake tsare dashi inda yayi Amfani da POS ya cire Naira Miliyan 35 ya baiwa ma'aikatan gidan yarin cin hanci dan su barshi yayi rayuwar jin dadi a gidan yarin. Basaraken kirikiri, Chief Babalola Shabi ne ya bayyana hakan a wajan wani taron karawa juna sani da hukumar 'yansandan jihar Legas ta shirya. Basaraken ya kara da cewa, Bobrisky be yi zaman gidan yarin da aka kaishi ba, maimakon hakan, an kaishi wani gidane a wajen gidan yarin bisa yaddar wasu gurbatattun ma'aikatan gidan yarin. Ya bayyana cewa da taimakonsa ne aka gano cewa Bobrisky bai yi zaman gidan yarin ba inda yace sai da ya tara masu sana'ar POS na yankinsa sannan ya kira hukumar EFCC dan ta bincika ta tabb...
Ƴanbindiga sun yi garkuwa da fiye da mutum 50 a Katsina

Ƴanbindiga sun yi garkuwa da fiye da mutum 50 a Katsina

Duk Labarai
Mazauna yankin ƙaramar hukumar Funtua ta jihar Katsina sun ce ƴanbindiga sun shiga wasu ƙauyukan yankin, inda suka kwashi Mutane sama da 50 da suka hada da mata da ƙananan yara. Maharan sun kuma kashe akalla mutum 6, inda suka sake kai wani hari a yankin karamar hukumar Dandume ta jihar. Rahotanni sun ce tun daga ranar Asabar maharan suka shiga yankin kuma ba su fita bah ar zuwa ranar Lahadi da rana. Malam Ya'u Ciɓauna mazaunin garin Layin Garaa ne na ƙaramar hukumar Funtua, kuma ya ce ''Misalin 10:30 na dare suka zo kuma sun kwashi maza da mata da ƴanmata da matan aure da kuma ƙananan yara har 53'' ''Sun kashe mutum 2 a Layin Garaa na ƙaramar hukumar Funtua da kuma wasu mutum 4 garin Mai Kwama a cikin ƙaramar hukumar Dandume.'' In ji Malam Ya'u. Shi ma maigarin Layin Garaa,...
Duk da farashin Danyen Man fetur ya fadi a kasuwanin Duniya, ‘yan kasuwar Man fetur na Najeriya sun bayyana dalilin da farashin man fetur din yaki sauka a Najeriya

Duk da farashin Danyen Man fetur ya fadi a kasuwanin Duniya, ‘yan kasuwar Man fetur na Najeriya sun bayyana dalilin da farashin man fetur din yaki sauka a Najeriya

Duk Labarai
Kungiyar masu tace man fetur na Najeriya, CORAN sun bayyana dalilin da yasa farashin man fetur ya ki sauka a Najeriya duk da farashin danyen man fetur ya sauka a kasuwannin Duniya. Sakataren yada labarai na CORAN, Eche Idoko ya bayyana cewa, dillalai dake tsakanin masu saye da masu sayar da man fetur dinne ke kawo matsalar hana farashin tashin sauka a Najeriya. Tun a makon da ya gabata ne dai muka kawo muku rahoton cewa, farashin na danyen man fetur a kasuwar Duniya ya sauka zuwa dala $65. Saidai a Najeriya, farashin ya ki sauka, da yake ci gaba da bayani, sakataren CORAN, Eche Idoko yace, idan ba dawo da ci gaba da sayarwa masu tace man fetur danyen man fetur din aka yi da kudin Naira ba, farashin man fetur din zai ci gaba da tashi ne. Yace amma matsalar itace, dillan man fet...